December 15, 2021

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 a sabuwar harin da suka kai Zariya

Daga Danjuma MakeryA wata sabuwar hari da yan bindiga suka kai garin Dallatu da kuma Kasuwar Da’a da ke yankin Dutsen Abba na karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna sun yi garkuwa da mutane 5 a yayin harin.

Wannan sabuwar harin da suka kai ta biyo bayan share awanni 24 kenan da harin da suka kai babban hanyar Kaduna-Zaria, inda suka kashe a kalla mutane 3, kana kuma suka yi awun gaba da wasu da dama.

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna bata fitar da rahoto kan faruwar lamarin ba, sai dai kuma a bangare guda mazauna yankunan sun bayyana cewa yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Dallatu da misalin karfe 1 na asubahin Laraba, kuma suka yi awun gaba da mutane 2.

Daga nan kuma suka kutsa kai zuwa kauyen Kasuwar Da’a inda suka yi awun gaba da mutane 6, wanda kuma 3 daga cikin su kananan yara ne.

Sai dai kuma wata majiya ta shaida cewa yaran 3 an sake su da safiyar yau Laraba, inda sauran mutane 5 din suka cigaba da kasancewa a sansanin ‘yan bindigan.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 a sabuwar harin da suka kai Zariya”