yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a Nigeria.

Rahotannin da aka ruwaito sun ce, jiya Asabar ne da yamma, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa da dama a lokacin da suka taso daga karamar hukumar Igueben zuwa Warri dake jihar Delta. Al’amarin ya sa na tuna irin garkuwar fasinjojin da wasu ‘yan bindiga suka yi a bara a layin dogon Abuja da Kaduna, labari ne ba dadi. Na taba ziyartar jihar Edo sau biyu a wasu shekaru da dama, wurin ya burge ni sosai, duk da cewa yawancin mazauna wajen ba sa magana da Hausa. Ina rokon Ubangiji Allah ya tona asirin wadanda suka kai harin. Allah ya bada zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ina kuma kira da a kara daukar matakai don tabbatar da tsaron fasinjojin layukan dogo a Najeriya. Amin.