September 7, 2021

Yan Bindiga Sun Sace Mutane 18 A Kaduna

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Rahotannin da suka zuwa mana daga unguwar Keke dake karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna na nuna cewa yan bindiga sun kutsa unguwar a talatainin daren jiya da misalin karfe 12 inda sukayi ta fitar da harsasai masu rai.

Shaidun gani-da-ido sun tabbatar da cewa yan bindigan sun zo ne ayari guda inda suka sanya mutanen yankin cikin halin dar inda kuma suka yi awun gaba da mutanen da adadin su bai gaza 18 ba.

A rahotannin da sukayita gabata sun nuna yankin ta Chikun tayi ta fama da matsalar yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

A watan Afrilun da ta gabata akayi garkuwa da dagacin Libere tare da iyalansa.
Kana a watan Fabrairu an sace wani adadi na mutane a yankin, duk karkashin kamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yan Bindiga Sun Sace Mutane 18 A Kaduna”