October 12, 2021

‘Yan bindiga sun sace dalibai a wata cibiyar “Darikar Katolika” a Kaduna

Daga Danjuma Makeri


Rahotannin da suke zuwa mana daga yankin masarautar Fadan Kagoma dake karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna na nuna cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar Saint Albertine dake karkashin kulawar darikar Katolika.

 

Wata majiya daga Fadan Kagoman ta bayyana cewa yan bindigan sun kutsa cikin makarantar ne da misalin karfe 10 na daren Litinin kana kuma suka fara ruwan harsasai.

 

Bayan farmakin nasu, yan bindigan sun yi awun gaba da wasu daga daliban makarantar wanda had zuwa yanzu ba’a san inda suke ba.

 

Hukumar ‘yan sanda na jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Yan bindiga sun sace dalibai a wata cibiyar “Darikar Katolika” a Kaduna”