December 15, 2021

Yan bindiga sun kashe dan majalisar jiha a harin babbar hanya ta Kaduna-Zaria

Daga Muhammad Bakir Muhammad


 

Rahotanni da ke zuwa mana daga jihar Kaduna na nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan matafiya a kan babban titin Kaduna da Zariya.

Rahoton ya tabbatar da rasuwar mutane wandanda a cikin su akwai wani dan majalisar jiha a Kaduna mai suna Alhaji Ridwanu Gadagau.

Alhaji Ridwanu Gadagau ya kasance Dan majalisar jiha mai waliktan yankin Giwa ta yamma dake jihar Kaduna.

Dan majalisar ya kasance daya daga cikin matafiyan da harin yan bindigan ya ritsa da su a kan babban titin Kaduna da Zariya a daren Litinin.

‘Yan bindigan dai sun kai harin me a daren Litinin inda suka shafe a kalla awanni 3, inda suka kashe wasu kana kuma suka yi garkuwa da wasu daga cikin su.

Rahotanni sun shaida cewa an tsinci gawar Alhaji Ridwanu ne a wata kauye da ke kusa.

Kakakin majalisar jiha a Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani ya tabbatar da rasuwar dan majalisa Ridwanu Gadagau ga manema labarai.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai ya fitar, ya bayyana cewa kakakin majalisa Zailani ya nuna tashin hankali da kuma radadin rashin dan majalisan.

Ya kuma Kara da cewa, kakakin majalisar ya jajantawa iyalan sauran jama’ar da ibtila’in ya ritsa da su.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yan bindiga sun kashe dan majalisar jiha a harin babbar hanya ta Kaduna-Zaria”