October 26, 2021

‘Yan bindiga sun kai hari mallaci, sun hallaka mutane 18 a Neja

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Rayukan mutanen da basu gaza 18 ba sun salwanta da safiyar jiya Litinin a yayin da yan bindiga suka kai hari a yankin Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu dake jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kai harin ne a bisa babura, inda kai tsaye suka nufi wata masallaci suka kashe mutane 18 a yayin da suke gudanar da sallar Asuba.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun wuce kai tsaye zuwa masallacin, inda suka kashe wasu mutane kana kuma suka yi garkuwa da su.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Yan bindiga sun kai hari mallaci, sun hallaka mutane 18 a Neja”