December 8, 2021

‘Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a Imo

Daga Danjuma Makery


Rahotonni na nuna cewa a kalla mutane biyu ne suka rasa raukan su kana kuma wasu kayayyaki da darajar su ta kai miliyoyin naira sun salwanta a yayin harin da yan bindiga suka kai Etekwuru da ke karamar hukumar Egbema ta Jihar Imo.

 

Rahotonnin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba.

Bayan salwantar rayuka da dukiya, wasu adadi daga mutanen kauyen sun jikkata, sai dai har ya zuwa yanzu ba’a san manufar ‘yan bindigan ba na kai hari kan yankin na Etekwuru.

Basarake mai sarautar gargajiya a yankin, Eze Kenneth Okereke ya tabbatar da faruwar harin da aka kai ga yan jaridu, kana kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da su kawo dauki kan talakawan sa, saboda kasantuwar ba wannan ne karo na farko da yan bindigan suka kawo hari yankin ba.

A watan Oktobar da ta gabata, wasu yan bindigan da har zuwa yau ba’a gane su wanene ba, sun farmaki gidan wata fadar sarauta a yankin, inda suka kone ta tare da motocin basaraken, kana kuma suka yi kokarin hallaka basaraken, sai dai kuma cikin taimakon ubangiji ya kubuta daga harin.

Inda a karshe basaraken ya rubuta takarda ga gwamnan jihar yana mai neman a kawo masa dauki, kana kuma cikin takardar ya bayyana cewa zai yi hijira zuwa wani wurin na daban.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a Imo”