September 28, 2021

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Sarkin Kagara


A yau Talata ne yan bindiga suka kai hari fadar Sarkin Kagara, Alhaji Ahmadu Attahiru a karamar hukumar Rafi da ke jahar Neja, sun kai farmakin ne a daren yau dai dai lokacin sallar Magriba.

Babu cikakken rahoto kan harin, amma mun samu labarin cewa a yayin da suka kai farmakin, Sarkin baya a fadar, rahoton ya ce Sarkin ya tafi halartar wani taro a garin Minna jiya Litinin.

Rashin samun cikakken rahoto daga garin na da alaka da katse layukan waya da aka yi a garin tun ranar juma’a.

An shaida mana cewa jami’an yan sanda na kan aikin bincike yanzu haka.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Sarkin Kagara”