YAKIN RASHA DA UKRAIN: Japan ta kakaba sabbin takunkumai ga kasar Rasha

Yan shekaru biyo bayan yakin da ya barke tsakanin kasashen Rasha da Ukrain da ke makobtaka da juna, kasar Japan ta sake kakabawa Rasha sabbin takunkumai kan abinda ta zarga a matsayin mamaya ga kasar Ukrain.
Takunkuman sun biyo bayan wasu tattaunawa guda bakwai da aka yi a birnin Hiroshima inda aka cimma matsayar neman karya karfin Rasha ta bangaren fasaha da kere-kere wadanda ke taimaka mata a bangaren yaki.
Sabbin takunkuman da Japan ta sanyawa Rasha sun hada da rike kayyakin Rasha da ke kasar Japan kana hakan ya shafi kaya mallakin gamayya ko daidaikun jama’ar Rasha. Kana an dakatar da fitar da kayayyaki ga duk ma’aikatun Rasha masu alaka da rundunar Soja. Kakakin gwamnatin kasar Japan Malam Hiroazu Matsuna shine ya shaiwa manena labarai hakan.
Kayayyakin da za’a rike sun hada da mallakin mutane 17 yan kasar Rasha da kuma na gamayya guda 78 wanda ciku akwai manyan masu mukami a rukunin sojin kasar Rasha.
Duk wannan matakai ne na ganin an cimma ga ci na sanya kasar Rasha kan gwiwowin ta da kuma mika wuya ga tarayyar turai. Sai dai a yayin da ake tufka ita ma kasar Rasha na warwara daga bangarenta