February 16, 2023

YAKIN KHAIBAR

 

Bayan yakin Ahzab (Khandak) ne labari ya zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) cewa akwai wani shiri na boye da ke gudana tsakanin Kuraishawa da Yahudawan Khaibara don yakar Musulmi. Sai Manzo (s.a.w.a) ya kuduri lallabar Kuraishawa don ya raba su da Yahudawa a matakin farko, don kuma ya sami daman yada kiransa a tsakanin Larabawa wadanda ba Kuraishawa a mataki na biyu.

Manzon (s.a.w.a) ya fuskanci Makka tare da mazaje dari biyar, inda suka isa Hudaibiyya. Sai Manzo ya aiki wani mutum daga kabilar Khuza’ah zuwa Kuraishawa don ya sanar da su cewa ya zo ziyarar Dakin Allah don yin Umara da soke hadaya a Harami, da cewa a shirye yake ya sa hannun zaman lafiya da su, in kuwa sun ki zai yake su.

Da ma Kuraishawa na fama da zafin galabarsu da aka yi a yakin Khandak; don haka da suka lura da irin karfin Manzo (s.a.w.a) da nacewarsa a kan abin da ya ke so, suka kuma riski irin raunin da suke fama da shi da gazawarsu a yaki, sai suka amsa kiran Manzo (s.a.w.a). Da haka aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu.

Alkawarin ya sami babban tasiri a tarihin ci-gaban Musulunci, yayin da ya bayar da dama ga Musulmi wajen isar da sakonsu ga wadanda ba Kuraishawa ba na daga mazauna tsibirin Larabawa, sannan suka sami sararin sabuwar gwamnatinsu da karfafa ta.

Khaibara wani gari ne daga garuruwan Yahudawa da ke makwabtaka da Madina. Garin na bisan dutse ne, an kewaye shi da ganuwar dutse, wanda ‘yan garin ke zaton za ta iya kare su daga takubban masu jihadin da ke samun taimakon Allah.

Yahudawan Khaibara suna da dabi’un sauran Yahudawa, rudin kai ya mamaye su, don haka Khaibara ta kasance wata cibiya ta kullawa musulmi makirci.

A ganuwar Khaibara akwai mayaki kimanin dubu goma, kullum suna fita sahu-sahu don yin atisaye, har suna yin izgili da irin karfin da Musulmi ke da shi suna masu cewa: “Mahammadu ne zai yake mu? Ko kusa!”

Manzon Alah (s.a.w.a) ya hada rundunarsa da azamarsa, ya kuma boye madosarsa. Ya bi hanyoyin da zai sa duk wani yunkurinsa ya zama cikin sirri, ya dogara da wasu masu nuna hanya. Don haka Yahudawa ba su sami wani labari ba sai bayan da Musulmi suka sauka a fagensu da daddare.

Lokacin da suka sami labarin isowar Musulmi sai shugabanninsu da masu fada-a-ji a cikin su suka yi taro don tsara hanyar da za su fitowa al’amarin da hana kai hari ganuwarsu.

Hari ya fara ne yayin da Manzo ya aiki halifa Abubakar “sai ya dawo ba tare da ya sami nasara alhali ya yi iya kokarinsa(3).

Tabari ya ce:

“Manzo Allah (s.a.w.a) ya bayar da tuta ga Umar dan Khaddabi, ya kuma hada shi da wasu mutane, suka je suka hadu da mutanen Khaibara, sai Umar da mutanen shi suka kasa suka dawo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) alhali mutanen da suka tafi da shi suna ragontar da shi shi kuma yana ragontar da su (wato kowa na razana dan’uwansa). Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: “Lallai zan bayar da tutar yaki gobe ga wani mutum da ke son Allah da ManzonSa kuma Allah da ManzonSa ke sonsa”. A wata ruwaya ta Ibni Hisham, Manzo ya kara da cewa: “Allah zai buda a hannunsa, shi ba mai gudu ba ne”. Da aka wayi gari, da ma Abubakar da Umar na ta sa rai ko su ne za a ba su wannan tuta, amma sai Manzo (s.a.w.a) ya kira Ali(4).

Sai ya ce masa: “Karbi wannan tuta ka tafi da ita har sai Allah ya bayar da nasara ta hannunka”.

Sai Ali (a.s) ya karbi tutar ya yunkura tare da wasu Musulmi, ya gabaci ganuwar Khaibara, sai wani shugaban Yahudawa ya fito tare da wasu mutane daga jama’arsa, ya yaki Ali (a.s) sai shi kuma (Ali) ya gaggauta sare shi a kai har sai da wadanda ke rundunar suka ji karar saran da aka yi masa(5)“.

Da haka Ali (a.s) ya bude kofar, duk wani kuzarin Yahudawan Khaibara ya wargaje daga nan, kuma Allah Ya ba ManzonSa nasara babba, aka watsa waccan runduna mai karfi.

www.ahlulbaiti.com

SHARE:
Makala 0 Replies to “YAKIN KHAIBAR”