September 24, 2021

Yakin Basra Ko Kuma Yakin Jamal (2)

Cigaba daga rubutun da ya gabata…A kan hanyarsu, sai ga labari ya zo wa wadannan ‘yan tawayen cewar Imam Ali (a.s) ya fito daga Madina ya nufo inda suke, don haka sai suka yanke shawarar bari asalin hanyar da suke kai suka dau barauniyar hanya zuwa Basra. Suna cikin tafiya kuwa sai suka zo wani waje mai dake tsakanin duwatsu ko kuma tuddai da ake ce ma Haw’ab, isowarsu ke da wuya sai wasu karnuka suka kewaye Ummul Muminina A’isha suka ta mata haushi da karfin gaske. Nan take sai hankalinta ya tashi, ta tambayi sunan wannan guri, jin cewa sunan wannan guri shi ne Haw’ab, sai hankalinta ya dada tashi, nan take ta tuna da gargadin da Manzon Allah (s) ya yi musu (matayensa) na su kiyaye tada fitina.

Sai ta dakata, ta sauko daga kan rakuminta, ta ce ba za ta ci gaba ba. Ganin haka sai Talha da Zubairu hankalinsu ya tashi, suna tunanin cewa burinsu ba zai cika ba. Don haka sai suka fito da wata hila inda suka ce wa A’isha sunan wannan guri ba Haw’ab ba ne, don ma su dada kwantar mata da hankali sai suka kawo wasu shaidu na zur (na karya) guda 50 suka rantse mata cewa ba sunan gurin ba kenan, amma duk da hakan dai ba ta yarda. Da suka ga hakan ma dai bai ci ba sai suka kirkiro wata hilar kuma inda suka ce mata labari ya zo cewa Ali ya kusan isowa don haka dole ne su bar gurin, jin hakan sai A’isha ta hau rakuminta suka ci gaba da tafiya.

Ko da suka isa Basra, sai Ummul Muminina A’isha, Talha da Zubairu suka fara tattaunawa da manyan mutanen garin da nufin samun goyon bayansu. Ta hakan dai sun sami goyon bayan wadansu mutanen, inda suka shiga garin suka kame gwamnan Imam Ali da ke garin wato Usmanbn Hunaif, bayan sun kashe wasu daga cikin masu gadinsa, bugu da kari kan kashe wasu daga cikin mabiya Ali (a.s). Daga karshe dai sun sami nasarar kame garin da kuma koran gwamnan barin sun wulakanta shi.

Labari dai ya zo wa Imam Ali (a.s) kan irin wannan tawaye da A’isha da Talha da Zubairu suka yi, don haka sai ya fara shirin fuskantar Basran, to sai dai da kyar ya tara sojoji kimanin 900 saboda kowa na jin nauyin fita don yakar A’isha wacce suka dauke ta a matsayin Uwar Muminai saboda kasancewarta matar Manzon Allah (s), baya ga haka kuma ga kokarin da Mu’awiyya shi ma ya yi na nuna wa mutane cewa Imam Ali (a.s) yana da hannu wajen kashe halifa Usman bn Affan.

A bangare guda kuma, Imam Ali (a.s) ya tura dansa Imam Hasan (a.s) da wasu daga cikin sahabbansa irinsu Ammar bn Yasir zuwa Kufa don tara sojojin, inda Imam Hasan din ya samu nasarar tara sojoji kimanin 9,000, baya ga wasu rundunoni kuma da suka dinga tuttudowa zuwa wajensa don yakan ‘yan tawayen da suka yi tawaye wa halaltaccen halifa.

Bayan da suka gama taruwa, sai Imam Ali (a.s) daga sansaninsa da ke Zhiqar ya rubuta wasika zuwa ga A’isha da Talha da Zubairu yana kiransu da su janye daga wannan tawaye nasu, amma dai suka ki yin hakan. Don haka sai ya kama hanya zuwa Basra don fuskantarsu tare da dakaru kimanin 20,000. A daidai lokacin kuma ita A’isha ta tara sojoji kimanin 30,000.

Ganin irin wannan runduna ta Imam Ali dai ta razana rundunar A’isha din. A nan ma dai Imam Ali (a.s) ya tattauna da su Talha da Zubairu don tabbatar da zaman lafiya, yana mai tunatar da su abubuwan da Manzon Allah (s) ya gaya musu a kansa inda duk suka amince sun ji wadannan maganganu. Zubairu dai ya ji kunya kwarai da gaske don haka sai ya bar gurin, amma shi Talha ya ki yarda, kamar yadda ita ma A’isha ta tsaya sai an yi yaki.

Da gari ya waye sai A’isha ta dare rakuminta ta umarci sojojinta da su shirin yaki. Haka yanayin ya yamutse, yaki ya balle tsakanin bangarorin biyu, inda musulmi suka yaki junansu a karo na farko. Wannan yaki dai shi ne yakin da ake kira da Harbul Jamal (Yakin Rakumi), saboda rakumin da A’isha ta kasance a kai yayin yakin.

Duk da cewa dai sojojin A’isha sun fi yawa, amma dai sun gagara samun wata nasara a kan sojojin Imam Ali, inda daga karshe dai dakarun Ali (a.s) suka yi nasara akan na A’isha, lokacin da aka raunana Talha, kana daga baya ya mutu, ita kuma A’isha aka kayar da rakumin nata. Ganin haka sai Imam Ali (a.s) ya umarci dan’uwanta Muhammad bn Abubakar da ya kula da ita kada wani abu ya same ta.

Bayan yakin ya kare, sojojin gaskiya sun yi nasara, sai Imam Ali (a.s) ya sanar da yin afuwa ga dukkan ‘yan tawayen, ya kuma hana dakarunsa diban ganimar yaki, ya koma sanya A’isha kan abin hawa aka koma da ita Madina.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Yakin Basra Ko Kuma Yakin Jamal (2)”