February 16, 2023

Yadda zaku gano inda wayar ku take idan an sace ta ko ta ɓata

 

Wannan rubutun akan wayoyin Android ne kawai. A rukunin “settings” na mafi yawancin wayoyin Android akwai option na “Security”, in ka shiga zaka ga rukunin da aka sa “Find My Device”, a wayoyi da dama za mu ga cewa a kunne yake “On”, in ba a kunne yake ba sai a kunna shi.

Duk sanda aka samu akasi irin yaran nan ƴan sara suka na gefen titi sun maka kwacen waya, ko kuma ka rasa inda wayar ka take, gida, kasuwa ko office, ko wani ya tsinta, zaka iya hawa shafin www.android.com akan computer ko kuma akan wata wayar, amma yafi sauƙin amfani a computer.

Idan shafin ya bude akwai option na “phones” menu na shafin da zaka zaɓa, daga nan sai ka gangaro ƙasa zaka ga “Support”, idan ka shiga nan zaka ga “Find My Device”, zai fito maka da inda za a bukaci sanya Gmail din ka da wasu bayanai na wayar ka, in ka saka komai daidai zai baka location din map na inda wayar ka take, tare da wuri na karshe da aka kunna ta ko akayi amfani da ita, har ma da motsin da ake yi da wayar daga nan zuwa can, duka zatayi maka tracking. Wannan zai taimaka maka wajen gano inda wayar ka take, kuma zai saukaka wa yan sanda bincike da gano inda za a kama mai laifin.

Ayi Sharing saboda amfanar jama’a.

Aliyu Samba
16/2/23

SHARE:
Tattaunawa 0 Replies to “Yadda zaku gano inda wayar ku take idan an sace ta ko ta ɓata”