July 28, 2021

YADDA TAFIYATA TA KASANCE DAGA DUNIYA ZUWA LAHIRA

YADDA TAFIYATA TA KASANCE DAGA DUNIYA ZUWA LAHIRA

 

Bayan na kammala sallar asuba ne, na samu karanta wani juzu’i daga littafin Allah (wato Al-Qur’ani) sannan naci abincin safe,na fita wajen aiki da sanyin safiya, isata keda wuya na samu ma’aikata suna jirana a kofar gareji, sun kasance suna sona, sannan suna girmamani sosai, kamar dai yadda suke fada nine injiniya daya dake kula da ma’aikatan sa, yake musu kyakykyawan tarba idan sunzo wurin sa. Na kasance ina farin ciki da hakan,kasancewa na hadimin su (Mai musu hidima), musamman masu yawan shekaru daga cikin su.

 

Haka nakasance na fito wajen aiki a wannan rana, Saidai tunda safe na kasance inajin wani abu dake damuna na rasa menene shi, har zuwa karfe daya na rana, na kasance ina zufa (gumi yana sauka daga jiki na) can sai naji wani ciwo da zafi tare da radadi a zuciyata…

Sai nayi tunanin abune na lokaci daya da zai wuce, take na nemi tsari daga Allah, saina bukaci da abani ruwan sanyi, a lokacin da nake shan ruwan sanyin kwatsam sai na fadi a kasa (Ni da kofin dake hannuna) nan take ma’aikatan masu kirki suka dauke ni da gaggawa zuwa asibiti…

Zuwan mu keda wuya likitoti suka karbe ni suka shigar dani wani daki…

Na kasance ina ganin duniya dishi-dishi a idona, sannan bana iya gane abu da sauri.

Bayan sunga halin da nake ciki ne sukayi waya da wani Dakta wanda ya iso da sauri domin duba halin da nake ciki, zuwan shi keda wuya ya sanya min wannan inji dake kula da bugun zuciya, zuciyata ta kasance tana bugawa da sauri, sannan numfashi na ya kasance shima yana fita da sauri ba yadda ya saba fita lokacin ina cikin koshin lafiyana ba, sannan gumi ya kasance yana sauka sosai daga goshi na.

Nan take naji ihun mai dakina tana kuka tare da rokon wadan nan dake kofa akan su bari ta shiga ta duba ni, sai naji daya daga cikin ma’aikatan yana ce mata wannan mara lafiya bazai yuwu a ganshi yanzu ba, domin ana kan masa aiki, Naso in bude bakina domin ince musu su barta ta shigo saboda akwai abinda nake son gaya mata, haka zalika naso azo min da ‘yayana domin in sumbace su sannan inyi musu wasici da juna, amma inaa babu wata fa’ida, domin a wannan lokacin harshe na ya mutu baya motsi bare in iya magana, sannan inaji kamar lokaci kadan ya rage inbar duniya.

Zuwa karfe biyar na yamma likitoti dayawa suka shigo guri na, a wani lokacin su kalle ni, wani lokacin kuma su juya suna kallon injin nan dake kula da bugun zuciyata, sunata magana wanda ina fahimtar wani amma bana iya fahimtar wani, domin na riga na rasa magana na tun farko, gashi yanzu ina kokarin rasa jina, babu abinda ya rage min sai gani na (Idanu na)  wanda naci gaba da tawassuli da wadan nan likitoti da subar matata ta shigo, koda na rabin dakika ne.

A wannan lokaci da nake gudu mutuwa tana biye dani, na iya tuna komai daya faru dani a rayuwata, dukkan marhaloli na gansu cikin idanu na, gani nan lokacin da nake karami mahaifiyata tana kula dani, ga kuma marhalan samarta wanda na ‘batata, ga kuma marhalan girma (lokacin da girma ya riga ya kamani) a yanzu kenan, hotunan rayuwan na gansu birjik cikin idanu na, na kasance ina tunawa ina kara tunawa, gani nan lokacin da nake karami, wani lokacin mahaifina yana umurtana da sallah, a wani lokacin inyi, wani lokacin kuma bazanyi ba, gani nan cikin abokai na muna cin zalin kananan yaran da basu kaimu ba, gani nan kuma wani lokaci na ‘bata ran mahaifiyata tana kuka duka saboda ni, gani nan kuma wani lokacin ina cin mutuncin matata saboda karya da kazafi da akayi mata…

Haka dai nayita nadama, nayi nadamar inama naji nasihan mahaifi na nayi sallah nayi azumi nayi da’a wa Allah tun farkon rayuwata…

saidai a yayin dana tuna na roke su sun yafe min sai naji wani sanyi a zuciyata.

Idanuna sun kasance suna kallon saman dakin da nake ciki, inata maimaita wasu kalmomi da ba wanda ke jinsu sai mahalicci na, inata maimaita cewa: ” _Ya ubangijina ka maidani cikin iyalaina zan bauta maka, inyi maka da’a irin yadda kake so”…_

Da misalin karfe takwas na dare daidai ne naga wani abu, wanda ban taba ganin irin saba a rayuwata, sai kawai aka dau raina daga wannan duniya zuwa wani wajen da bansan inane ba.

Nan kuwa ‘yan uwana suka dauke ni zuwa gidana suka ajiye ni a tsakiyan gida suna kuka, ai kuwa kawo ni keda wuya sai ‘yayana suka zo kaina suka kuka tare da ihu, sun kasance suna kuka mai tsanani, suna kuka suna kiran mahaifin mu ka tashi, a cikin su harda karamar ‘yata, data kasance a kullum tana jiran dawowa na domin in kawo mata alawa in dauketa ina yi mata wasa, sai gashi yau (a irin wannan dare) tazo kan gawa na tana kuka bazan iya amfanar da ita da komai ba bare in rarrashe ta, matata da ‘yan uwana tare da makota sun kasance suna kuka, duka wadanda suka halarci gidana sun kasance suna kuka suna kiran sunana, saidai ni na shagala da wani abun wanda bazan iya sifanta shi ba, ina cikin wani halin da bata tasu nake ba.

Haka nan suka dauke ni domin suyi min wanka, bayan sunyi min wanka ne suka sanya min likafani na, sannan suka sanya gawana cikin mota domin su kaini gidana na gaskiya, nan da nan muka isa karbala, sai suka dauke ni zuwa makwancin Aba Abdullah (AS) a nanne naji nutsuwa, sai nayi amfani da wannan damar na fara tawassuli da jirgin tsira (iyalan manzo) (S), ina kiran inama su zamto masu ceto na a wajen Allah, ina tawassulin ina kuka mai tsanani, ina tuna lokacin da nake zuwa majilisin ashura tare da ‘yayana, ammafa duka kukan nan da nake, da tawassul mutanen dake tare dani basa ji, dukda cewa ina daga muryana sosai.

Bayan nanne motar ta nufi najaf al’ashraf, sai naga sun shigar da gawana zuwa makwancin Imam Ali (AS) anan sukayi min sallar janaza, ni kuwa na kasance ina tawassuli da Amirul-mu’uminin (AS) domin ya cece ni, haka nan ya roka min Allah yaji qaina.

Bayan nan ne suka tafi dani zuwa waadis-salam (Wanda ni na kasance mai yawan ziyaran makabarta) amma a wannan lokacin sai naga ziyaran yasha bamban da irin ziyaran da na kasance inayi, lokuta dayawa na kasance ina ziyartan kabarin mahaifina tare da karanta masa abinda ya sawwaka daga kur’ani, sannan na koma gida da wuri babu bata lokaci, amma a wannan lokaci sai na fahimci ni za’a bari anan (daga ni sai abinda na aikata) har zuwa ranar kiyama.

Nan take suka sanya ni cikin wani rami ina mai fuskantar alkibla,suna kuka, sukayi min addu’oi (wanda sun dau lokaci suna wannan kukan) bayan nanne suka tafi dukkan su suka barni ni kadai na.

Kabarin ya kasance mai duhu kuma abin tsoro wanda bazai yuwu in sifanta shi ba,haka nan isowan mala’ikun nan biyu ya kara firgita ni, nanfa suka fara yi min tambayoyi. Waye ubangijin ka? Saina amsa da: Allah ne ubangiji na. Suka kara tambayana. Waye Annabin ka? Sai na amsa musu da: Annabi Muhammad (S) shine Annabi na, sai suka kara tambaya na.  Waye Imamin ka? Saina amsa da cewa: Ali da ‘yayan shi ma’asumai sune imamai na…Haka nan sukayita tambaya na ina basu amsa cikin tsoro da firgici, a hankali a hankali sai naga cikin kabarin yana haske, har zuwa lokacin da sallah na da zakkah na da kumusi na suka zo suka rinka kareni daga tambayoyin da ake min…

Can sai ga wani saurayi kyakykyawa yazo, sai yayi min sallama yace min: “Nine kyautatawan daka kasance kana yiwa mutane, kada kaji tsoro”.

Na zauna a kabari na lokaci mai tsawo, har zuwa lokacin da mai aukuwa ta auku (kiyama ta tashi) wanda a gaskiya ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba, domin sama ta tsatstsage, taurari kuma sun tarwatse, kogi yayi ambaliya, kaburbura sun tottone, shi kuma Mala’ika israafil ya hura kaho sau daya, nan take dukkan rayuka suka tattara a mahallin hisabi…

Kafurai suna ihu, sun kasance suna cewa: ” _Wannan wane irin tashin hankali ne, kuma inane nan”_ sai suji an amsa musu da cewa _:”Wannan shine alkawarin ubangijin ku, sannan ‘yan aiken ubangijin ku sunyi gaskiya” Annabawan Allah da ‘yan aike da Imaman tsira sun kasance suna shaida akan abinda aka aiko su dashi._

Ana haka kuwa sai aka tsaida ni domin hisabi, aka rinka bincike na akan babba da karami na ayyukan dana aikata, na tsinci kaina a cikin wani halin tsoro da tashin hankali irin wanda dutse bazai iya dauka ba, saboda nauyi, musamman a lokacin da naga kyawawan ayyukana sunyi daidai da munanan ayyuka na…

Nan dai na tsaya babu kaya a jiki na, a kaskance, a wasu lokutan nakanyi dubi zuwa ga dama na, a wasu lokutan kuma zuwa ga hagu na, sauran mutane suna cikin wani yanayi daban da yanayin da nake ciki, a ranar ne naga mutum yana gudun dan uwan sa, yana gudun mahaifin sa da mahaifiyar sa…

Gashi ni bansan ya makomata zata kasance ba…

har zuwa lokacin da ceton Ahlul-baiti (AS) ya shafe ni, sai aka dauke ni aka sanya ni cikin ma’abota dama, aka tafi dani zuwa aljannah, wannan lokaci shine lokacin da naji dadin da ban taba jin irin sa ba, saina gane ashe wannan shi ake kira da tsira na hakika, tsira daga wuta zuwa aljannah.

Amma masu aikata sa’bo an sanya su cikin rundunan ma’abota hagu, sun kasance suna ihu suna kuka babu wani mai tausayin su, can sai kaji kiran ubangiji cewa: _(Ku kama su ku daure su, sannan ku sanya su cikin wutar jahim, a cikin sarƙoƙi, wanda tsayinsa kamu saba’in ne…_

Na shiga Aljannah naga wasu da nasani, na samu mahaifina da mahaifiya ta, haka nan na samu malami na da ya kasance yana nuna min hanyar tsira, na same su suna kan daraja mai girma, mala’iku suna yi musu hidima, koramu suna gudana a kasansu, muka kasance masu farin ciki da jin dadi, tare da godewa ubangijin mu daya cika alkawarin da yayiwa wadanda sukayi masa da’a, nan na gane “Ashe wannan ake kira ceton Ahlul-baiti (AS)”

 

Imrana Darussalam

28/July/2021

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “YADDA TAFIYATA TA KASANCE DAGA DUNIYA ZUWA LAHIRA”