January 10, 2024

Yadda Ta Kasance Kan Shari’ar Zaben gwamnan Adamawa A Kotun Koli

Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP Dr Umar Ardo, ya shigar kan zaben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Ardo ya garzaya kotun kolin ne yana neman ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa,wanda kotun daukaka kara ta tabbatar.

Wanda ya shigar da kara ya bukaci kotun ta soke zaben da ya ayyana Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa saboda rashin bin dokar zabe.

Kotun daukaka kara dai ta yanke hukuncin korar karar ne,inda tace wadanda suka shigar da karar ba su tabbatar da zargin almundahana da rashin bin dokar zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Yadda Ta Kasance Kan Shari’ar Zaben gwamnan Adamawa A Kotun Koli”