October 2, 2023

Yadda ta kasance a Ganawar Kungiyoyin Kwadago da Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago sun cimma matsaya kan dakatar da yajin aikin da kungiyar ta shirya yi a fadin kasar bayan wata ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja.

shugaban kungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero ya ce N25,000 da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar a jawabin cikar Nigeria shekaru 63 da samun ‘yancin kai zai fara aiki ne ga dukkanin ma’aikata mai makon kananan ma’aikata da aka fada a baya, Kuma ya kara Naira 10,000 ya koma Naira 35,000.

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta amince za ta cire kaso 7.5% na haraji, VAT da ake biyawa man dizal domin tabbatar da rage farashin kayayyakin da ake amfani da su, wanda dama da shi ne kamfanoni suke amfani wajen samar da wutar lantarki a masana’antu da ofisoshi.

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta amince za ta cire kaso 7.5% na haraji, VAT da ake biyawa man dizal domin tabbatar da rage farashin kayayyakin da ake amfani da su, wanda dama da shi ne kamfanoni suke amfani wajen samar da wutar lantarki a masana’antu da ofisoshi

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yadda ta kasance a Ganawar Kungiyoyin Kwadago da Gwamnatin Najeriya”