January 3, 2023

Yadda sunan Coca-Cola ya samo asali.

Daga Saliaddin Sicey

 

Mai yiwuwa ka taba jin cewa lemon Coca-Cola na dauke da wasu sinadarai wadanda ke iya sa mutune su riƙa matuƙar sha’awar shan sa: wato hodar iblis. (Cocaine) 🍾Sunan Coca ya samo asali ne daga ganyen coca inda mutumin daya ƙirkiro lemon John Pemberton, dake sayar da magunguna a birnin Atlanta ya hada ganyen goro da ruwan sukari. 🍾A wancan lokacin a farkon ƙarni a 19, an saba harhada ganyen coca da giya kuma dubarar Pemberton wajen hada sukari wata hanya ce ta kaucewa dokoki da suka haramta sayar da barasa A Zamanin. 🍾Amma a bangare guda kuma sunan yana nufin sauran kayayyaki da ba’a san su ba amma kuma suna da ƙarfi sosai- wato goro. ɓawon goron idan baka taɓa gani bai kai tsawon inci biyu ba kuma launin shudi ne. Cikin sa yana yin jajaja, ko kuma fari-fari. 🍾A ƙasashen yammacin Afrika, masu cin goro sun maida shi wani abu da ke ƙara musu kuzari. 🍾Saboda ƙwallon ya na dauke da sinarin caffeine da theobromine, wadanda ake samu a ganyen gahawa da kuma chakulan. 🍾Har ma suna dauke da sukari a cikin su 🍾Yan kasuwa kan dauki goro akai su yi tafiya mai nesa saboda muhimmancinsa. 🍾Akwai wasu abubuwa da za’a dauka kai tsaye a cikin su, kuma an kwashe shekaru aru-aru ana noman goro a ƙasashen yammacin Afrika. 🍾Masana tarihi irin su Paul Lovejoy sun ce cikin shekaru da dama an fara shuka ganyen goro ne a ƙaburbura domin yin tsafi na lokacin da mutum ya isa matsayin balaga. 🍾Koda yake ana buƙatar irin da ake shukawa ya kasance yana da damshi-damshi, a wasu lokuta yana da wahalar girbi inda ‘yan kasuwa kan yi dogon kafiya a ƙasa daga gonaki a cikin tsakiyar daji. Koda yake yadda ake ajiye goro ya danganta ga yadda matsayin goro ya ke ga al’umma. 🍾A shekarar 1581, Sarkin daular Songhai a yankin yammacin Sahel ya aike da wasu kyaututtuka zuwa wajen bukin gina masallaci a birnin Timbuktu, kuma kayayyakin sun hada da gwal da wuri, wato (cowrie shells) a turance da kuma goro. 🍾Daga ƙarni a 19, an fara fitar da tan-tan na goro zuwa nahiyar turai da Amurka. Su dai turawa basu san goro ba kwata-kwata sai daga ƙarni na 15 lokacin da jiragen ruwa na turawan Portugal suka iso gabar tekun ƙasar Saliyo, in ji Lovejoy. 🍾Kuma yayin da turawan suka shiga kasuwancin goro har suka fara fitar da goro ta teku, a shekarar 1620, lokacin da baturen Ingila Richard Jobson ya shiga Gambia, goro wani sabon abu ne a wajen shi. “Ya rubutu cewa a lokacin da mu ke bakin teku, mutane su kan kawo mana tulin goro kuma mu a lokacin bamu damu da shi ba,”. 🍾”Guda goma kyauta ce ta sarki.” A lokacin da aka ba shi manyan-manyan goro guda shida, Robson ya yi fatan cewa zai koma da su Ingila, sai dai sun bushe ko kuma tsutsa ta cinye kafin ya isa gida. 🍾Koda yake wannan rashin sani bai dauki dogon lokaci ba, domin kuwa a ƙarni na 19, an fara fitar da tan-tan na goro zuwa nahiyar turai da Amurka. 🍾Kuma galibin wadanda ake shigo da su nahiyar ana amfani da su ne wajen harhada magunguna a kamfanoni kamar su Burroughs Wellcome and Co’s da kuma “Forced March” tablets, wadanda ake yi domin ƙara kuzari. 🍾”Suna dauke ne da wasu sinadarai dake cikin goro ko kuma ganyen Coca,” kuma ana zayyana su a bayan maganin. 🍾Wani maganin da ake sha daya shahara shi ne Vin Mariani, da ake yi daga ƙasar Faransa wanda ya ƙunshi ganyen coca da aka hada da giya. Wanda ya fara yin magani ne shine Angelo Mariani, dan kasar Faransa a shekarar 1863 kuma Paparoma Leo XIII na matuƙar sha’awar maganin har an riƙa sanya hoton sa a tallar maganin na Vin Mariani. 🍾Sauran wasu fitattun mutane da aka ce suna sha’awar maganin sun hada da Sarauniya Victoria da Thomas Edison da kuma Arthur Conan Doyle. 🍾Amma wannan magani daya ne daga cikin magungunan dake sanya kuzari da ake da su a lokacin da ake ganin tasirin sinadarin yana da girma sosai. 🍾A don haka lokacin da Pemberton, dan ƙasar Amurka dake sayar da magunguna ya hada wannan sinadari, shine na baya baya da ake ganin tasirin sa. 🍾Kuma yayin da hodar iblis ya daina tasiri a matsayin sinadarin da ake amfani domin ƙara kuzari, tasirin lemon da ake yi da ganyen kola sai ya ƙara ƙaruwa. A yanzu bayanan sinadaren da ake harhada Coca-Cola abu ne da ake matuƙar boyewa, koda yake an ce lemon baya dauke da sinadarin goro. 🍾Kusan za’a a ce a yanzu ana sayar da lemon “Coca-Cola kimanin biliyan daya da miliyan dari tara a kowace rana a duniya. 🍾Lemon ya shahara da har wani yunkuri na neman a sauya masa dandano a shekarar 1985 ta hanyar ƙara masa zaƙi a wani mataki na neman ƙarin kasuwa ya haifar da mummunar sakamako, inda masu sha’awar lemon suka yi ta bayyana fushin su, lamarin daya sa tilas aka maido da shi yadda yake 🍾Nasarar da Coca-Cola ya samu ya taimaka wajen sa kamfanin ya kasance abu na uku da yafi suna a duniya. 🍾A yanzu dai bayanan sinadaren da ake harhada Coca-Cola abu ne da ake matuƙar boyewa, sai dai lemon baya dauke da sinadarin goro, a maimakon haka an samun wasu abubuwa ne masu dandano do suka kama da yadda lemon yake a shekarun baya. 🍾Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi Nemi The little known nut that gave Coca-Cola its name.

SHARE:
Noma da Kiwo 0 Replies to “Yadda sunan Coca-Cola ya samo asali.”