June 2, 2024

Ya Allah kajikan Imam Khumaini Ruhullah (Ks) 1

Wafatinsa da rabuwa da masoya, haduwa da abin kauna Hakika Imam Khumaini ya isar da abin da yake son fadi da kuma cimma abin da yake son cimmawa tsawon rayuwarsa a aikace. Don haka a halin yanzu cikin tsakiyar watan Khordad 1368 (farko-farkon watan Yuni shekarar1989) yana ta kan shirye-shiryen ganawa da Abin kaunarsa da ya gudanar da dukkan rayuwarsa don neman yardarSa. Wanda ya kasance bai taba mika kai ga wani bayanSa ba, kamar yadda bai taba zubar da hawaye ba sai don Shi, sannan kuma dukkan wakokin irfanin da ya rera (ko rubutawa) sun kasance suna bayanin kan dacin rabuwa da Abin kauna da kuma shaukin da yake yi na saduwa da Shi. A halin yanzu da lokacin yake gabatowa, duk da cewa abu ne da masoyansa ba za su iya jurewa ba, ya rubuta cikin wasiyyarsa cewa: “Ina muku sallama ‘yan’uwana maza da mata, cikin kwanciyar hankali da rai mai natsuwa da ruhi mai farin ciki da zuciya mai fatan falalar Allah, in kama hanya zuwa ga gidana na har abada. Kuma ina mai matukar bukatar addu’arku ta alheri. Sannan ina rokon Allah Mai rahama da jin kai Ya karbi uzurina na karancin hidima da kurakurai da gazawa. Kuma ina fata jama’a za su karbi uzurina cikin kowane karanci na hidima da kurakurai da gazawa, kuma su ci gaba da karfi tare da kakkarfar aniya..

Babban abin ban al’ajabin shi ne cewa tun kafin shekaru da rasuwarsa, Imam Khumaini, cikin wasu baitocin wake ya yi batun rasuwarsa cikin watan Khordad inda yake cewa: Shekaru suna wucewa abubuwa suna ta faruwa Ni kuwa ina sauraron nasara a tsakiyan Khordad

Daidai karfe sha daya da minti ashirin na dare ranar asabar 13 ga watan Khordad shekarar 1368 (3 ga Yuni shekarar 1989) lokacin saduwa da abin kauna ya yi. A daidai wannan lokaci ne zuciyar da ta haskaka zukatan miliyoyi da hasken Allah ta tsaya cak (ta bar aiki). A daidai wannan lokaci masoya Imam sun boye wata kamara (na’urar daukan hoto) a asibitin da yake kwance don daukan abubuwan da ke gudana da aikin da aka masa har zuwa lokacin saduwa da abin kauna. Don haka lokacin da gidan talabijin din Iran ya nuna halin kwanciyar hankalin da Imam ya ke ciki a lokacin, kai kace zukatan al’umma za su fashe saboda shaukin da ba za a iya siffanta shi ba.

A lokacin lebbansa cike suke da ambaton Allah, a daren karshe na rayuwarsa ma’abuciya daukaka a daidai lokacin da dantsensa yake daure da alluran da ake kara masa ruwa, amma sai ga shi ya mike don sallar dare da kuma karatun Alkur’ani mai girma. A daidai sa’oin karshe na rayuwarsa, ba abin da ake gani face kwanciyar hankali da nitsuwa ta Ubangiji yana mai ikirari da kadaitakan Ubangiji da imani da sakon Manzo (s.a.w.a) har lokacin da aka dauki ransa zuwa wajen Ubangijinsa. Wannan rasuwa da ta rura wutan bakin ciki a zukata. Lokacin da aka watsa labarin rasuwar Imam, kai ka ce wata gagarumar girgizar kasa ce ta faru, ko ina sai bakin ciki idanuwa kuwa a cikin Iran da sauran wuraren da aka san Imam kana kuma shiriyarsa ta shiga sai zubar da hawaye suke. Masoyansa sai fitowa suke suna dukan kawuka da fuskokinsu da alkaluma da duk wani irin bayani ya zaga wajen bayyana hakikanin abubuwan da suka faru da irin bakin cikin da ake ciki. Lalle mutanen Iran da sauran ma’abuta juyi suna da hakkin yin irin wannan kururuwa da tarihi bai taba ganin irin girma da tsananinsa ba, don kuwa sun rasa wani masoyi ne da ya dawo musu da mutumci da daukakan da suka rasa, sannan ya katse hannayen muggan shugabanni da ‘yan mulkin mallakan Amurka da sauran kasashen yammaci daga kasashensu, sannan kuma ya raya Musulunci da hakkokin musulmi da mutumcinsu, ya kuma tsai da Jamhuriyar Musulunci, ya tsaya kyam a gaban karfin shaidan don fuskantar darurrukan makirce-makircensu na kawar da gwamnatin Musulunci da haifar da fitinar cikin gida da waje tsawon shekaru goma. Kamar yadda kuma ya jagoranci yakin kariya na shekaru takwas yana fuskantar makiyan da suke samun goyon bayan gwamnatocin gabashi da yammaci ma’abuta girman kai. Hakika al’umma sun rasa jagoransu abin kauna sannan kuma makomarsu na addini kana kuma mai kira zuwa ga Musulunci na hakika

Mai yiyuwa ne mutanen da suka gagara fahimtar hakikanin wannan lamari su kasance cikin rudani lokacin da – gidan talabijin ya nuna – halin da mutane suke ciki yayin jana’iza da bisne jikin Imam mai tsarki. Mai yiyuwa ne su sha mamaki lokacin da suka ji labarin rasuwar mutane masu yawa da suka gagara jurewa wannan babban rashi don haka zuciyarsu ta tsaya cak ko kuma na faduwar wasu gomomin mutane sakamakon tsananin bakin ciki da dai sauran abubuwa makamantan haka da suka faru. Sai dai mutanen da suka san ma’anar kauna kana kuma zukatansu suka ta’allaka da shi cikin sauki za su iya fahimtar lamarin da kuma ganinsa ba a bakin komai ba. A hakikanin gaskiya al’ummar Iran sun kasance masu tsananin kaunar Imam Khumaini, don haka yayin zagayowar shekarar rasuwarsa suke rera taken: “Kaunar Khumaini kaunar dukkan abubuwa masu kyau ne”.

®Fatima Mohammed

Zamuci gaba

SHARE:
Labaran Duniya, Raruwar Magabata, Tsokaci 0 Replies to “Ya Allah kajikan Imam Khumaini Ruhullah (Ks) 1”