January 12, 2024

YAƘININ MATASHI A BISA IMANINSA !

Marubuci: Malam Al-Baqir Ibrahim Saminaka

An rawaito daga Al-Imamus Sadiƙ (A) cewa: Wata rana Manzon Allah (S) a masallaci bayan idar da sallar asuba, dab da zai bar masallacin sai ga wani matashi kansa sunkuye, jikinsa a sanyaye, alamu sun nuna yana cikin tsananin damuwa ne…. Sai Manzon Allah (S) ya tambaye shi: “Yaya ka wayi gari?”. Ya amsa “Na wayi gari ina mai yaƙini ne ya Ma’aikin Allah” Cike da mamaki Manzon Allah ya sake tambayar sa “Lallai kowane yaƙiƙi yana da haƙiƙaninsa, to kai mene ne haƙiƙanin naka yaƙinin?”

 

A saiɓance wannan matashi ya ce: “Ya Ma’aikin Allah, haƙiƙa yaƙinina shi ne ya sanya ni damuwa, shi ya hana ni barcin darena, ya kuma sanya ni jin ƙishi da rana, don hana na gudar da kaina (Na ɗauke tunanina) daga duniya da abinda ke yikinta. Ina kwatanta hango al’arshin Ubangijina an ajiye shi (An zo) don yin hisabi, ga halittu duk sun taru saboda haka ni ma ina cikinsu, kamar ga ni ina hango ƴan Aljanna sun morewa a cikin Aljannar suna gagganawa da junansu, zazzaune a ƙawatattun wurare cikin ni’ima, ga kuma kamar ina hango ƴan wuta ana yi musu azaba, suna ta -kururuwar- neman ɗauki da agaji. Yanzu ɗin nan tamkar ina jin ƙugin ne wutan a kunnuwa ne”

 

Sai Manzon Allah (S) ya juya wajen Sahabbansa ya ce: “Lallai wannan bawa ne wanda Allah ya haska zuciyarsa da imani” Sannan ya yi wasici wa wannan matashi cewa “Ka riƙe wannan abinda da kake a kan shi da kyau!” Sai matashin ya ya ce: “Ya Ma’aikin Allah ka yi mini addu’a in samu Shahada a tare da kai” Sai Annabi (S) ya yi masa addu’ar kuma ya samu Shahadar.

— [Al-Kāfiy: 2/53]

 

____________

D A R A S I !

N FARKO: A wannan ƙissa, mun gani a bayyane irin yadda Manzon Allah (S) ba ya sakaci da al’ummarsa da halin da suke ciki, dubi yadda cikin jama’a har ya iya gano wani mutum wanda yake cikin damuwa, dubi yadda ya fuskance shi cikin tausasawa don jin ko mece ce damuwarsa. (Wannan ga iyaye, da ma duk wani na sama) Sau nawa kake kula ka gane na ƙarƙashinka yana cikin damuwa? Ta yaya kake raɓar shi don jin damuwar ta shi…?

 

NA BIYU: Kamr yadda Manzon Allah (S) ya faɗi “Kowane yaƙini yana da haƙiƙaninsa” Tambayar farko ga kaina ita ce: «Wai ma mene ne yaƙin nan? Shin ni ina da shi ma kuwa?» na bazama neman yaƙinina… A yayin da na samu cewa ina da yaƙini, a nan tambaya ta biyu kuma «To ni kuma mene ne haƙiƙanin nawa yaƙinin?» Dole dai yana haƙiƙa (tushe), ko da kuwa abin so ne ko akasi. Don haka, dole na tashi na yi aiki tuƙuru don inganta tushen Imanina. Lallai ban ga ta zama ba!

SHARE:
Makala 0 Replies to “YAƘININ MATASHI A BISA IMANINSA !”