April 16, 2023

Wulakanta Al-kur’ani Mai Girma Wani Nau’i Ne Na Ta’addanci Da Tunzura Mutane

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kan’ani ya bayyana cewa wulakanta ko kona littafi mai tsarki na Musulmi wani nau’I ne na ta’addanci da kuma tunzura musulmi wadanda suke girmama shi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naser Kan’ani yana fadar haka bayan da wata kungiya mai tsatsauran ra’ayin kin addinin musulunci ta kona Al-Kur’ani mai girma a birnin Copenhagen na kasar Denmark. Banda haka sun kuna tutar kasar Turkiyya wacce mafi yawan mutanen kasar Musulmi ne.

Kan’ani ya kara da cewa wannan kungiyar mai tsananin kiyayya ga addinin musulmice da musulmi ta aikata haka ne a ranar Jumma’an da ta gabata, kuma a cikin watan Ramadan watan da musulmi suka yi imani a cikinsa ne aka fara saukar da alkur’ani mai girma.

Wannan ya faru a dai-dai lokacinda suka san cewa mutane kimani biliyon 2 a duniya suna girmama shi.

A wani bangare kuma ranar Jumma’a da ta gabata ce ranar Qudus ta duniya inda musulmi suke kokawa kan yadda yahudawan sahyoniya shekaru fiye da 70 da suka gabata suke mamaye da kasar Falasdinu, suna kuma kashesu da kuma korarsu daga gidajensu da kuma kasarsu ta haihuwa.

Wannan shi mummunan fahintar encin dadin albarkacin baki wanda kasashen yamma suke iddi’ai kuma suke alfahari da shi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Wulakanta Al-kur’ani Mai Girma Wani Nau’i Ne Na Ta’addanci Da Tunzura Mutane”