WHO, Ta Bukaci A Ceto Yanayin Kiwon Lafiya A Falasdinu.

Kudurin da ya samu karbuwa da gagarimin rinjaye ya mayar da hankali ne kan magance bukatun kiwon lafiyar jama’a a yankunan Falasdinu da aka mamaye.
A wannan kudirin a bukaci gwamnatin Isra’ila ta tabbatar da hanyar da hanyoyin da suka dace domin baiwa motocin daukar marasa lafiya na Falasdinu shiga inda ya kamata, da kuma mutuntawa da kare lafiyar ma’aikatan kiwon lafiya, kamar yadda ka’idojin jin kai na kasa da kasa suka tanada.
Kudurin ya kuma bukaci hukumar lafiya ta Duniya da ta taimaka wajen inganta tsarin kiwon falasdinu, da samar da alluran rigakafi, da magunguna da kayayyakin aikin jinya, da tabbatar da adalci wajen samun lafiya a yankunan da aka mamaye.