Wata sabuwa: Kotu ta kara soke zaben fid da gwanin gwamna na PDP a Zamfara, tare da haramta wa PDP shiga cikin zaben gwamna a 2023 a jihar

Wata sabuwa: Kotu ta kara soke zaben fid da gwanin gwamna na PDP a Zamfara, tare da haramta wa PDP shiga cikin zaben gwamna a 2023 a jihar
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau babban birnin jihar Zamfara ta soke zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP.
Zaben fitar da gwani na baya-bayan nan da aka gudanar a jihar ya bai wa Dauda Lawal-Dare nasara a kan abokan takararsa.
Mai shari’a Aminu Bappa ya kuma yanke hukunci cewa jam’iyyar PDP ba za ta tsayar da dan takarar gwamna a jihar ba a zaben badi da ke tafe.
Wannan dai shi ne karo na biyu da kotu ke soke zaben fitar da gwani da jam’iyyar ke gudanarwa a jihar ta Zamfara.
A watan Satumba ma kotun ta soke zaben fid da gwanin wanda Lawal-Dare ya lashe, sakamakon korafe-korafen da wasu ‘yan takara suka shigar gabanta suka kalubalantar sahihancin zaben.
Kotun ta umarci da a sake gudanar da wani zaben a watan na Satumban, inda kuma Lawal-Dare ya sake yin nasara.