April 2, 2024

Wata mahaukaciyar guguwa ta afkawa arewacin Madagascar

Wata mahaukaciyar guguwa ta afkawa arewacin Madagascar

Guguwar da ta afkawa arewacin Madagascar a ranar Larabar da ta gabata ta yi sanadin mutuwar mutane akalla shida tare da tilastawa wasu 2,000 barin gidajensu.

Rahotannin cikin gida na cewa ” ambaliyar ruwa ta haifar da babbar illa ” tare da lalata hanyoyi da gadoji.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato hukumar kula da bala’o’i (BNGRC), ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon guguwar Gamane ya kai 11.

An bayyana cewa shida daga cikin wadanda abin ya rutsa da su sun nutse, yayin da sauran kuma suka mutu bayan fadowar bishiyu ko rushewar gidaje.

“Abu ne mai wuya a sami guguwa irin wannan, motsinta ya kusa tsayawa,” in ji Janar Elack Andriakaja, babban darektan BNGRC.

“Lokacin da tsarin ya tsaya a wuri guda, yana lalata dukkan ababen more rayuwa. Kuma hakan na da mummunan sakamako ga yawan jama’a. da gagarumin ambaliya.”

#Madagascar

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Wata mahaukaciyar guguwa ta afkawa arewacin Madagascar”