March 22, 2023

wasu ‘yan tawaye a gabashin Jamhuriyar demokaradiyyar Congo, sun halaka fararen hula a kalla 21.

Farhan Haq, mataimakin mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, wasu ‘yan tawaye a gabashin Jamhuriyar demokaradiyyar Congo, sun halaka fararen hula a kalla 21 a karshen mako.
A cewarsa, a cikin makonni biyu da suka gabata, hare-haren ‘yan tawayen Allied Democratic Forces (ADF) sun yi sanadin mutuwar fararen hula a kalla 118.
Haq ya bayyana cewa, tawagar wanzar da zaman lafiya a DRC, wadda aka fi sani da MONUSCO, ta ba da rahoton wasu hare-hare da aka kai a yankunan arewacin Kivu da Ituri da ke makwabtaka da su cikin daren ranar Asabar, lamarin da ya raba jama’a da muhallansu.
Kakakin ya ce, dakarun tsaron na MONUSCO da na DRC, sun kaddamar da sintiri na hadin gwiwa a kan hanyar Beni-Butembo, a matsayin mayar da martani, tare da yin hadin gwiwa da hukumomin yankin da sauran al’umma a yankunan da ‘yan tawayen ADF ke rike da su.
Ya bayyana cewa, a kalla fararen hula 11 ne suka mutu a arewacin lardin Ituri, ciki har da mata biyu da kananan yara biyu, a wani samame da kungiyar CODECO mai dauke da makamai suka kai a kauyuka da dama a yankin Mahagi. Yana mai cewa, an tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kauyen Ngote don gudanar da sintiri, a wani mataki na kare rayukan fararen hula dake gujewa tashin hankali da kuma tallafawa kokarin da sojojin kasar ke yi, na dawo da kwanciyar hankali.

© (Ibrahim)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “wasu ‘yan tawaye a gabashin Jamhuriyar demokaradiyyar Congo, sun halaka fararen hula a kalla 21.”