December 9, 2022

Wasu ‘yan majalisar dattijai sun gargadi babban bankin Nijeriya kan shirinsa na rage adadin kudin da al’umma za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar Phillip Aduda ya janyo hankalin wakilan majalisar kan cewa matakin na CBN zai yi illa ga al’umma musamman ma masu ƙananan sana’o’i.

A nasa tsokacin, shugaban majalisar sanata Ahmed Lawan ya ja hankalin bankin na CBN da ya yi nazari kan lamarin kafin yanke hukunci kai-tsaye, kasancewar matakin zai shafi mutane da dama.

Ya kuma ce akwai bukatar a tattauna da bankin domin samun cikakken bayani kan tsarin, sannan ya bukaci kwamitin kula da harkar bankuna na majalisar ya tattauna kan batun a lokacin zaman tantance mataimakan shugaban bankin, wanda ake sa ran yi a mako mai zuwa.

A karkashin sabon tsarin na CBN, ɗaiɗaikun mutane na da damar cire naira 100,000 ne kacal a mako, yayin da kamfanoni za su iya cire naira 500,000 a mako.

A kan wannan dai Majalisar dattawan ta yi sammacin wasu mataimakan gwamnoni biyu na babban bankin Najeriya da su bayyana gabanta a gobe Juma’a domin yin cikakken bayani kan dokar takaita fitar da kudade da babban bankin ya bayyana a ranar Talatar da ta gabata

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Wasu ‘yan majalisar dattijai sun gargadi babban bankin Nijeriya kan shirinsa na rage adadin kudin da al’umma za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu.”