September 8, 2023

Wasu tagwayen hare-haren ta’addanci da aka kai a Mali sun halaka fafaren hula 49 da sojoji 15

An kai wasu hare-haren ta’addanci guda biyu a kasar, inda aka auna wani jirgin ruwan fasinja da kuma wani sansanin soji dake arewacin kasar, lamarin da ya haddasa kisan mutane 64, da suka hada da fararen hula 49 da sojoji 15. Mahukuntan kasar Mali sun sanar da zaman makoki na kwanaki uku tun daga Jumma’ar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, wata kungiya mai alaka da al-Qa’ida ta yi ikirarin kai wadannan hare-hare.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Wasu tagwayen hare-haren ta’addanci da aka kai a Mali sun halaka fafaren hula 49 da sojoji 15”