September 5, 2021

Wasu ƴan Zamfara sun fara gudun hijira zuwa Kano bayan katse layukan wayar tarho

Daga Baba Abdulƙadir
Al’ummar jihar Zamfara na cigaba da bayyana irin yadda su ka tsinci kan su bayan da aka katse layukan wayar salula a fadin jihar domin shawo kan matsalar tsaro da ke ci gaba da yaduwa tamkar wutar daji.
A hirarmu da wani mazaunin jihar mai suna Murtala Muhammad Bello Gusau, da ya yo gudun hijira daga jihar ta Zamfara zuwa Kano ya bayyana cewa a halin yanzu rayuwa a jihar Zamfara ta koma tamkar a zamanin da.
Ya ƙara da cewa babu wani abu da ake iya aiwatarwa musamman wanda ya shafi sadarwa sakamakon katse layukan sadarwar da aka yi. Ya ce hatta tura kudi da kuma tuntubar mutum domin jin lafiyarsa ko kuma a yi zumunci ya gagara.
Haka kuma Murtala Bello Gusau, ya ƙara da cewa a yanzu idan mutum ya je neman wani bai same shi to zaɓi na ƙarshe shi ne ya jira shi ko kuma ya bar masa rubutaccen sako ta hanyar gajeruwar wasika.
Ita ma wata matashiryar yar kasuwa da ta buƙaci mu sakaye sunanta ta bayyana cewa sakamakon katse layukan sadarwar ya sanya tai yo gudun hijira zuwa Kano domin ji ta ke tamkar a lahira ta ke zaune.
“Gaskiya ba zan iya zama a inda babu sabis ɗin waya ba musamman saboda irin yanayin kasuwancin da na ke yi. Domin ina aikewa da kayayyaki zuwa Abuja da Kaduna, ka ga kuwa tilas in dawo Kano domin cigaba da kasuwanci na”
“Kuma gaskiya daga lokacin da aka katse layukan tarho din zuwa wani ɗan lokaci sai na ji tamkar a wata duniyar mu ke ba wacce mu ka saba ba”
A jiya Asabar ne dai hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta NCC ta katse layukan wayar tarho a jihar ta zamfara bayan da ta samu takardar bukatar yin hakan daga Gwamnan Jihar Muhammad Bello Matawalle.
Jihar Zamfara dai na cikin jihohin da suke fi fama da tashin hanaklin ƴan bindiga da ƴan fashin daji da kan yi garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Wasu ƴan Zamfara sun fara gudun hijira zuwa Kano bayan katse layukan wayar tarho”