April 9, 2023

WASIYYOYIN SHEIKH HABIB KAZIMY DOMIN RAYA DARAREN LAILATUL QADRI

 

1 – Ka sami hutu da yamma domin samun ƙarfin ibada da dare.

2 – Ka kasance cikin shiri domin tuba, kafin raya daren da bayan sa.

3 – Ku yawaita karanta du’a faraj na Imamul-Hujjah (Atfs).

4 – Yi kokarin tuban zuciya da yin kuka, domin su biyun sune shugabannin ladduba na addu’a.

5 – Ka guji kai ƙaran wani, ka yafema wanda ya zalunce ka.

6 – Ka maida hankali akan yanayin yadda ayyukan suke, ba muhimmi shine ka kammala raka’a ɗarin nan ba, alhali zuciyan ka bai shirya karbar tuba ba.

7 – Ka kasance a cikin tsarki tsawon wannan dare, ka fara da wanka.

8 – Kayi yaƙinin amsa maka addu’oin ka, domin rashin yaƙinin amsa addu’a ya iya samar da hijabi.

9 – Marairaicewa a yayin addu’a, domin mala’iku sukan duba sautin bawa.

10 – Kayi munajati da Allah da zuciya mai rauni, sannan ka tattaro dukkan munanan ayyukan ka, da munanan da kake aikatawa, ka tabbatar masa kaine kake aikata su, amma yanzu kana nadama.

11 – Yawaita Istigfari da salatin Annabi da iyalan gidan sa tsarkaka.

12 – Ka maida hankali akan muhimman addu’oi, domin masu ƴantarwa ne daga wuta, da samun kusanci da Allah a aljanna.

13 – Ka ruƙi buƙatun ka da cikin su akwai amfanin duniya da lahira (kamar arzikin halal, da mace ta gari, da ƴaƴaye nagari, da makamantansu) wanda zasu taimake ka a duniyar ka da lahirar ka.

14 – Ya kamata kayi sujjada mai tsawo, domin Annabi (S) a hudubar sa shahararriya yake cewa: ….Ku sani Allah maɗaukaki ya rantse da izzar sa cewa bazai azabtar da masu sallah da sujjada ba.

15 – Ka ribatu da kowane daƙiƙa, na haneka gazawa, domin kyautuka a wannan dare suna da yawa, kada ka wadatu da kaɗan.

16 – Ka raya wannan dare har zuwa fitowar alfijir, a sanda mala’iku suke halin hawa da sauƙa.

17 – Ka godewa Allah akan ni’iman raya wannan dare na lailatul-Qadr, domin wani sashe daga mutane sun gafala da wannan dare, wasu kuma suna fursuna ana azabtar dasu, wasu kuma suna gadon rashin lafiya, ka samar da dogon sujjada keɓantacciya domin godiyawa Allah akan wannan ni’ima da ya baka.

18 – Kada ka mance sadakan da zata nunku maka, ka tuna da faƙirai da mabuƙata.

19 – Yana daga muhimmin aiki a daren lailatul-Qadr “Neman ilimi” babu laifi muɗala’ar litattafan akhlaq da zasu gyara maka ruhi da litattafan Aqeeda.

20 – Kada ku manta iyaye, ƴan uwa, abokai, maƙota, abokan aiki, malaman mu, ƙasar mu a cikin addu’oin ku.

 

©Sheikh Emran Darussalam.

SHARE:
Makala 0 Replies to “WASIYYOYIN SHEIKH HABIB KAZIMY DOMIN RAYA DARAREN LAILATUL QADRI”