Wasiyoyi 12 Daga Sayyid Ali Khamene’i (DZ) Domin Amfanuwa A Dararen Lailatul-Qadr:

1 – Kuyi shiri (ma’anawi) domin raya daren lailatul-Qadri kafin zuwan shi.
2 – Ku amfana da lokutan lailatul-Qadri, sannan kusan girman shi.
3 – Ku nisanci dukkan nau’oin munanan ayyuka māādi, musamman mummunan aikin da ya kasance fasadi ne ko zalunci.
4 – Addu’a shine mafificin aiki a wannan dare, da raya (daren) da sallah zikiri domin addu’a.
5 – Ku kula da ma’anan addu’oin ma’asumai yadda lafazin yake maikyau da ma’ana mai zurfi.
6 – Ku magantu da Allah kai tsaye, ku nema a gurin sa, domin babu hijabi tsakanin ku da shi.
7 – Ku nemi uzuri a gurin Allah maɗaukaki daga dukkan zunuban ku, da siffofi marasa kyau, da gazawan ku.
8 – Ku tunatar ma kanku girman muƙami na Amirul-muminin (AS).
9 – Ku magantu da Imamin zamanin ku (fansar ran mu gareshi) kai tsaye, sannan ku roƙi Allah ya baku domin albarkan shi.
10 – Kuyi dogon nazari cikin ayoyin halitta da makomar mutum a duniya da lahira.
11 – Addu’oin ku ya kamata ya shafi lamarin da ya shafi ƙasa da dukkanin musulmi.
12 – Ku roƙi Allah madaukaki dukkanin buƙatun ku, da buƙatun sauran muminai, da sauran mutanen da ake azabtar dasu (wadanda ake zalunta).
Nima Emran Darussalam kada ku manta dani cikin addu’oin ku.
©13/04/2023.
Emran Darussalam.