November 22, 2022

Wani mutum ya nemi taimako domin kula da ‘ya’yansa 200 da jikoki 567

Kafafen yaɗa labaran Uganda sun ce wani ɗan ƙasar ya nemi taimako domin kula da ‘ya’yansa 200, sakamakon matansa 12 sun rabu da shi da kuma matsin tattalin arziki da yake fuskanta.

Musa Hasahya – wanda ya ce shi ɗan kasuwa ne – ya buƙaci gwamnati da ƙungiyoyim bayar da tallafi su agaza masa wajen tura ƙananan yaransa zuwa makaranta.

Ya ce ya mallaki dukiyar da ta isa ya ciyar da iyalansa, amma ilimi ya yi tsada matuƙa.

Haka kuma mutumin ya ce yana da jikoki kusan 567 da suma ke ƙarƙashoin kulawarsa.

©Bbc Hausa

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Wani mutum ya nemi taimako domin kula da ‘ya’yansa 200 da jikoki 567”