September 29, 2021

Wani Mutum Ya Kashe ‘Dansa Mai Shekara Biyu A Bayelsa

Daga Abdussalam AlabiWani mutum mai suna Vwede ya hallaka d’an shi har lahira ta hanyar duka kana kuma ya tsere, hakan ya faru ne a garin Yenagoa da ke jahar Bayelsa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi a kan titin Imiringi da ke Yenagoa wanda ya ja cece-kuce tsakanin makobta da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama.

Rahoton ya nuna cewa mahaifin yaron yayi wa yaron bugu mai tsanani sannan kuma ya dauke shi zuwa Asibiti a sume.

Amma ba da jigawa ba mahaifin ya tsere bayan ma’aikatan sun tabbatar masa da cewa yaron ya mutu.

Mai magana da yawun yan sandan jahar Bayelsa SP Asinim Butswat ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya kuma ce mahaifin ya tsere wanda ya zuwa yanzu ba’a san inda yake ba.

Tun farkon lamarin dai wasu daga lauyoyi masu kare hakkokin yara da mata sun nuna bacin ran su akan faruwar lamarin.

Bayan faruwar lamarin mazauna yankin sun kai rahoto zuwa ga ofishin yan sanda na Akenfa, sai dai a lokacin da aka kai rahoton mahaifin yaron ya riga ya tsere.

Ya zuwa yanzu yan sanda na bincike kan lamarin don gano inda mahaifin yaron ya tsere domin kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Wani Mutum Ya Kashe ‘Dansa Mai Shekara Biyu A Bayelsa”