October 14, 2021

Wani matashi ya kashe kansa a jihar Ilorin

Daga Isah Musa Muhammad


A jiya Laraba ne wani matashi mazaunin Ogidi a Ilorin, babban birnin jihar Ilorin ya kashe kansa har lahira.

An tsinci gawar matashin ne a wani kango tana rataye a rufin wani bangare na kangon, inda mazauna unguwar suka tsinke igiyar da ke daure a wuyansa kana kuma suka sauko da gawar sa.

Mazauna unguwar sun shaida cewa mamacin ya tube kayansa inda dan kamfai ne kawai ya saura jikin sa kafin ya kashe kan nasa.

Ya zuwa yanzu ba’an san dalilin da ya sanya matashin ya hallaka kansa ba, amma wasu daga mazauna yankin sun tabbatar da cewa matashin ya dau tsahon lokaci yana korafe-korafe kan wahalhalu da yake fuskanta a rayuwar sa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Wani matashi ya kashe kansa a jihar Ilorin”