October 17, 2021

Wani matashi ya hallaka tsoho dan shekaru 50 a Ogun

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Hukumar yan sandan jihar Ogun ta damke wani matashi dan shekaru 25 mai suna Bisi Omoniyi da laifin kashe abokin takarar sa Akinyemi Wahab Alani.

‘Yan sandan sun cafke matashin ne biyo bayan kiran da suka samu a ofishin su na Owode Egbado, inda aka kira su aka basu rahoton cewa wani matashi ya kashe wani tsoho a garin Ajilete da ke karamar hukumar Yewa a jahar Ogun.

Mai magana da yawun yan sandan, Abimbola Oyeyemi ya shaidawa manema labarai a garin Abeokuta cewa bayan kiran da aka yi musu ne DPO Owode Egbado ya shirya yan sanda ya alike su zuwa inda lamarin ya faru domin kama mai laifin.

Jami’in ya shaida cewa ba tare da wani bata lokaci ba suka dauki dattijon zuwa asibiti amma kuma bayan isar su aka shaida musu cewa ya mutu.

Jami’in ya bayyana cewa a binciken da suka yi sun gane cewa wanda ya aikata laifin da kuma mamacin dukkan su suna da alaka ta soyayya da wata mata mai suna Kafayat Sakariyau, bincike kuma ya nuna cewa mamacin ya ziyarci Kafayat a daren da lamarin ya faru, bayan yan wasu sa’o’i shi ma Bisi ya ziyarci gidan saidai kuma an hana shi shiga, a wannan yanayin ne Bisi ya shiga dakin da karfin tsiya inda kuma ya iske su a wani yanayi da bai yi masa dadi ba.

Jami’in ya bayyana cewa wannan dalilin ne ya haifar da sa’in’sa tsakanin mamacin da kuma matashin inda a yayin fada matashin ya dauki makami ya kuma kashe tsohon har lahira.

Jami’in ya ce gawar mamacin an ajiye ta a dakin ajiyan gawarwaki a asibiti, a bangare kuwa its Kafayat ta yi layar zana tun bayan faruwar lamarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Wani matashi ya hallaka tsoho dan shekaru 50 a Ogun”