April 17, 2023

Wani Dan Bindiga Dadi Ya kashe Mutane 4 A Kasar Amurka

 

Majiyar ‘yan sandan Jihar Alabama ta Amurka ta sanar da cewa, an kashe mutane 4 bayan da wani dan bindiga ya bude musu wuta, yayin da wasu mutane 20 kuma su ka jikkata.

Kakakin ‘yan sandan jihar ta Alabama Jeremy Burkett ne ya sanar da manema labaru hakan, yana mai kara da cewa; An bude wutar ne a wurin bikin zagayowar haihuwar wani.

Kafafen watsa labarun yankin da lamarin ya faru sun ce, mahalarta taron matasa ne, kuma tuni an dauki wadanda su ka jikkata zuwa asibiti.

Kafar watsa labaru ta “W.R.B.L” ta ce tuni jami’an tsaro su ka zagaye wurin da lamarin ya faru.

Kashe mutane ta wannan irin hanyar da daidaikun mutane ke bude wuta, wani abu ne da ya zama ruwan dare a kasar Amurka.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Wani Dan Bindiga Dadi Ya kashe Mutane 4 A Kasar Amurka”