May 9, 2023

​Wakilan Bangarorin Rikicin Sudan Na Ci Gaba Da Tattaunawa A Saudiyya

 

Hankula sun karkata zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya, inda ake tattaunawa da nufin kawo karshen tashe-tashen hankula a Sudan tare da bude hanyar warware rikicin ta hanyoyi na siyasa.

Tattaunawar da Babban Kwamishinan Agaji na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya shiga, na da nufin duba batutuwan jin kai da suka shafi Sudan.

Tattaunawar da ake yi a Jeddah ta zo ne a cikin tsarin wani shiri na Saudiyya da Amurka, wanda shi ne yunkurin farko mai na a zo a gani na kawo karshen fadan da ake yi tsakanin sojojin da dakarun RSF, wanda ya mayar da sassan babban birnin kasar Khartoum, zama yanki na yaki.

Kwamandan rundunar RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya tabbatar da shiga cikin tattaunawar da kungiyar ta sa, kuma yana fatan za ta cimma burin da ta sa a gaba, wato bude wata hanya mai kyau ga fararen hula.

Hukumomin cikin gida, da bangarori daban-daban na yanki da na Larabawa, da kuma Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka, da kuma kungiyar raya kasashe masu tasowa sun yi maraba da wannan ci gaba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Wakilan Bangarorin Rikicin Sudan Na Ci Gaba Da Tattaunawa A Saudiyya”