Wahabiyanci A Mizani Kashi na daya ( 1).

Wahabiyanci da wanda ya assasashi:
– Ana nasabta firƙan wahabiyya ne ga Muhammad bin Abdulwahab Bn Sulaiman Annajdi, wanda aka haifa a shekarar 1115 Hijiriyya, ya rasu a shekarar 1206 Hijiriyya.
Yayi karatun addini daidai gwargwado, kamar yadda a bayyane yake ya kasance mai yawan bibiya da muɗala’an labaran da suka shafi Musailama al-kazzab, da Sajah, da Aswadul Anasi, da Ɗulaiha Al-asadi, wanda tsatstsauran ra’ayin shi ya fara bayyana tun lokacin da yake karatu, mahaifin sa da wasu daga malaman sa su suka fara yaƙar wannan ra’ayi nashi, suka nuna a nisance shi, inda suke cewa: “Wannan zai ɓata, kuma zai ɓatar da dukkan waɗanda suka nisanci Allah kuma suka kasance shaƙiyyai”.
A shekarar 1143 Hijiriyya ya bayyana da’awar sa zuwa ga sabuwar mazhabin sa, amma mahaifin sa da wasu daga malaman sa suka yi ƙoƙarin tsaida shi tare da tunkarar sa, suka karya karsashin kiran nasa, har zuwa lokacin da mahaifinsa ya rasu a shekarar 1153 Hijiriyya, a nanne ya samu damar jaddada da’awar sa tsakanin masu ƙarancin ilimi, da sauran mutane, aka samu dayawa daga cikin su suka bishi, nan mutanen garin suka taso kan shi (saboda yadda suka ga yana ɓatar da mutane) suka yi ƙoƙarin kashe shi, a lokacin ne ya gudu wani gari da ake kira (Uyainah), bayan zuwan shine ya samu kusantar sarkin Uyainah ya auri ƴar uwar sa, ya zauna a nan yana kira zuwa ga kanshi kuma zuwa ga bidi’ar sa, har ta kaiga ya ƙure haƙurin mutanen Uyainah suka kore shi daga garin, haka ya fita zuwa (Addar’iyyah) dake kan hanyar Najid.
Haka fikirar sa ta yaɗu a wannan gari har sarkin garin Muhammad bn Mas’ud ya zama daga mabiyan wannan tafiya tashi da sauran mutane, haka yaci gaba da tasarrufi kamar ma’abocin ijitihadi muɗlaqa, domin kuwa bai kasance yana ɗaukan fatwan magabata (Salaf) ba, kuma baya ɗaukan fatwan faƙihan zamanin sa, dukda a haƙiƙanin gaskiya bayyi karatun da ya kaishi ga ijitihadi ba.
Amma ɗan uwan sa Sheikh Sulaiman bn Abdulwahab ya sifanta shi, wanda shi yafi kowa sanin sa, wanda ya kaiga rubuta littafi guda domin ɓata kiran ɗan uwan shi da tabbatar da hatsarin ta tsakanin al’umma, kamar yadda yazo a wani ibaara inda yake bayyana ta’arifin wahabiyya da wanda ya assasa ta, inda yake cewa: “A yau an jarabci mutane da wanda ke intisaabi zuwa ga kitabu wassunnah, yana istinbaɗi (tsamo hukunce-hukunce) a cikin ta ba tare da ya damu ba, wanda ya saɓa dashi a ra’ayi sunan shi kafuri, wanda kuma a haƙiƙanin gaskiya babu wani alama na ijitihadi data bayyana tare dashi, amma dukda haka ya saye ƙwaƙwalen dayawa daga jahilai, innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.
Masdar: zaka samu duka wannan da ƙarin bayani a:
– تاريخ نجد لمحمود شكري الآلوسي.
– الصواعق الإلهية في الرد على الوهابية للشيخ سليمان بن عبد الوهاب.
– فتنة الوهابية.
©Sheikh Emran Haruna Darussalam.