Wafatin Sayyida Khadija Al-Kubra (AS).
Yana Daga Karamar Sayyida Khadija Al-Kubra (S).
Cewa:
Sayyid Sadiq Shirazi ya naƙalto cewa: Wasu ma’abota ilimi sun hakaito masa wannan ƙissa cewa:
Na kasance ina duba littafin dake da alaƙa da Sayyida Khadija Al-Kubra (S) amma bansamu ba, duk da cewa na duba shi sosai amma bansamu ba, sai ta bayyana min cewa babu wani tsayayyen littafi da rubuta shi da sunan ta, sai naji babu daɗi, ta yaya har zuwa yanzu ace babu littafi da aka rubuta shi musamman da sunan wannan shaksiyya mai girma, bayan naga littafin da aka rubuta musamman da sunan Fidda khadimar Sayyida Zahra (S).
Wata rana sai na haɗu da aboki na Sheikh Ghalib Sailawi, yana ɗaya daga cikin manya-manyan marubutan iraqi, sai na kai masa kuka na kan wannan batu, nace masa: Idan ka iya yin wani abu akan wannan batu zaka samu lada mai yawa.
Shaikh Sailawi ya amsa bukatata, nan yayi ƙoƙari har ya samu nasarar wallafa littafi akan Sayyida Khadija a watanni 6, aka buga littafin Alhmdlh.
Sheikh Ghalib yace: bayan na kammala wallafa littafin ne wani abu yazo min a zuciya nake cewa Sayyida Khadija haƙiƙa na kammala miki littafin ki, bari naga me zakiyi.
Sheikh ya ƙara da cewa: A wannan daren ne kuwa aka kira ni a waya, a yayin da na ɗaga sai naji mutumin dake maganar bansan shi ba, sai ya tambaye ni: Shin kaine marubucin littafi kaza?
Na amsa da eh.
Yace: Meyasa ka rubuta sunan ka a bangon littafin ba tare da ka sanya kalmar (Hajj ba) Alhaji.
Nace: Saboda banje ɗakin Allah ba.
Yace: Meyasa bakaje ba!
Nace: Saboda bana da kuɗin zuwa.
Yace: Ina haɗaka da Allah gobe kazo Tehran a guri kaza zan baka kuɗin da zasu ishe ka zuwa hajji.
Haka kuwa akayi a washe gari naje inda ya ambata na karɓi kuɗin, sannan Allah ya ƙaddara min abokin da muka tafi tare dashi zuwa makkatul-mukarrama.
Haka Sheikh Ghalib Sailawi ya samu tasharrufin zuwa hajji a wannan shekara, ina biye dashi, Wataran Sheikh yace min: Ina son inje ziyarar ƙabarin Abu-Taleb (AS), muka tsaida alƙawari mukaje, a sanda muka je sai naga ya ɗaga hannu sama da littafi, sai na tambaye shi: Sai yace wannan littafin Shugaba tace Sayyida Khadija (AS).
Nace: me kake yi dashi?
Yace nazo na kawo mata shi hadiyya ne.
Ayatullah Rohollah Koemaini (QS) yake cewa: “Kuna yawan cewa ita babar Imamai goma sha ɗaya ne, amma a haƙiƙanin gaskiya ita babar Imamai 12 ce, domin ita babar Imam Ali (AS) ce, domin Amirul-muminin (AS) ya samu tarbiyya da raino daga gurin ta.
Ina taya ɗaukacin al’ummar musulmi baƙin cikin kewayowan wannan rana na shahadar Sayyida Khadija (AS)
©Sheikh Imran Haruna Darussalam.