October 21, 2021

Uwar gidan shugaban Turkiyya ta kaddamar da cibiyar al’adu a Abuja

Daga Mustopha Abdulfathi


Uwar gidan shugaban kasar Turkiyya, Emine Erdogan a jiya Laraba ta kaddamar da “Yunus Emre Institute” a birnin Abuja wanda ya kasance cibiyar al’adun Turkiyya.

Ta samu rakiya da taimakawar mai dakin mataimakin shugaban kasar Nijeriya Mrs. Dolapo Osinbajo, da kuma Ministan jin ‘kai Haj. Sadiya Umar Faruk.

Uwar gidan shugaban kasar Turkiyya, Emine ta bayyana cewa bude wannan cibiyar ya kasance ne don karfafa alaka da mu’amala ta al’adu tsakanin kasashen guda biyu.

 

Cibiyar an sanya mata sunan shahararren mawakin karni na 13, Yunus Emre. Kana kuma cibiyar zata zama bisa yada al’adun Turkiyya da kuma yaren Turkish da kuma fadada bangarorin ilimin kimiyya da fasaha.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Uwar gidan shugaban Turkiyya ta kaddamar da cibiyar al’adu a Abuja”