Shirin koyo da koyarwa daga gida a tsakanin dalibai da malamai a Kano bai cigaba yadda ake zato ba.

Asusun lura da kananan yara na MDD na UNICEF ya ce, har yau shirinsa na koyo da koyarwa daga gida ta amfani da na’urar kwamfutar IPAD a tsakanin dalibai da malamai a jihar Kano bai ga cigaban da ake zato ba.
Asusun na UNICEF ya ce a tsakanin watanni shida da suka gabata, kasa da 1% kawai aka samu kwatankwacin dalibai 1280 ke nan suke amfani da manhajar a jihar ta Kano dake arewacin Najeriya.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da Karin bayani.
Babbar jami’ar dake lura da ofishin UNICEF a jihar Kano Rahma Rihood Farah ce ta tabbatar da hakan a jiya Asabar 6 ga wata, yayin da take mika kayayyakin tallafawa shirin karatu ta amfani da na’urar kwamfutar IPAD ga hukumar lura da ilimin bai daya ta jihar Kano SUBEB.
Jami’ar ta ce burin asusun na UNICEF shi ne zuwa watan Disambar wannan shekara, masu amfani da wannan manhajar karatu su kai dubu 75, sannan kuma zuwa karshen shekarar 2024 su kai miliyan 1.5.
Mrs Rahama Farah ta ci gaba da cewa, Asusun na UNICEF yana aikin hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya a Najeriya, karkashin wannan shiri kamar yadda yarjejeniyar take, gwamnatoci za su yi kokarin wadata makarantu da na’urorin kari a kan wanda asusun ya samar a matsayin tallafin sa musamman a jihohin da aka kaddamar da shirin.
Malam Naziru Sirajo shi ne jagoran kula da yadda shirin ke gudana a jihar Kano ya yi mun karin haske game da shirin da kuma adadin yawan kayan da asusun na UNICEF ya ba su karkashin shirin.
“Wannan wani sabon tsari ne da aka kawo a Najeriya ta yadda dalibi zai iya koyon karatu a gida ta amfani da internet ko kuma kai tsaye daga cikin kundin dake kunshe da darussa daban daban da aka adana a na’urar kwamfutar IPAD, wanda yanzu jihar kano tana daga cikin jihohin da suka dace da wannan tagomashi daga asusun na UNICEF, inda ya ba da kwamfutar hannu ta tablet guda 1,430, sannan kuma an ba mu na’urar routers guda 75 sai na’urar majigi wato Projector guda 100, wanda mun raba su a cikin makarantun da aka kayyade, kuma muna iya kokarin ganin cewa dukkan makarantun sun amfana kuma sun yi amfani da kayan bisa dalilan da suka sanya aka samar da su.”
Manufar dai wannan shiri shi ne saukakawa malamai hanyoyin koyarwa, sannan za a iya koyar da yaro ta hanyar magana kawai ko kuma ta hanyar hoto da mai magana wanda wannan zai kara kaifafa basirar dalibai da saurin fahimtar darussa cikin nishadi.
(Garba Abdullahi Bagwai)