September 16, 2023

​UAE: Ba A Cire Takunkumin Biza A Kan ‘Yan Najeriya Ba

 

Wasu majiyoyi na gwamnatin UAE sun tabbatar da cewa, har yanzu kasar ba ta janye takunkumin hana ‘yan Najeriya bizar shiga kasar ba.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai wasu rahotanni daga fadar shugaban Najerya sun ce a wata tattanawa da aka yi tsakanin Tinubu na Najeriya da Muhammad Bin Zayid na UAE, sun cimma matsaya kan janye takunkumin hana ‘yan Najeriya bizar shiga UAE.

Gwamnatin kasar ta UAE dai a cikin wata sanatwa a watan Oktoban shekarar da ta gabata ta bayyana cewa ta dakatar da bayar da takardar biza ga ƴan Najeriya da wasu ƙasashen Afirika guda 19. Ƙasar ba ta kuma bayar da ƙarin bayanai. An kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin ƙasashen biyu bayan kamfanin jirgin Emirates ya tsayar da ayyukansa bisa dalilin an riƙe masa kuɗaɗensa a Najeriya.

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta ce babu wani lokaci da aka tsaida domin jiragen sama su cigaba da jigilar daga Najeriya zuwa UAE. Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa cigaba da aikin kamfanonin Emirates da Etihad ba zai zama da wuri, amma ba kamar yadda aka fada ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​UAE: Ba A Cire Takunkumin Biza A Kan ‘Yan Najeriya Ba”