August 3, 2021

TUNJI DISU YA MAYE GURBIN ABBA KYARI

Daga Muhammad Bakir Muhammad

A ranar Litinin, 2 ga watan Agusta Sufeto Janar na ‘yan sanda ya nada Tunji Disu matsayin sabon kwamandan Rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da manyan laifuka a kasar don maye gurbin tsohon Mataimakin kwamishinan ‘yan Sanda Abba kyari wanda ya kasance mai jagorantar rundunar kafin nadin Tunji Disu. Dakatar da Abba Kyari din dai ya biyo bayan zarginsa da ake na karbar cin hanci daga Hushpuppi; mutumin da ake zargi da laifin damfara.

Kafin nadin sa, Disu ya yi aiki da hukuma ta musamman kan magance matsalolin tsaro  wacce ake kira da “Rapid Response Squad” a turance inda ya taka rawar gani sosai wurin dakile matsalonin tsaro musamman a garin Legas.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “TUNJI DISU YA MAYE GURBIN ABBA KYARI”