Tsohon Shugaban kasar sudan Umar Al Bashir na Sudan ba a san inda yake ba Bayan An Fasa Kurkukun da Yake Daure A Cikin sa.

A wata sanarwa da Ahmed Haroun ya fitar ya ce shi da wasu tsoffin jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir sun tsere daga gidan yarin Kober.
An shiga tambayar inda tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya shiga a ranar Laraba, 26 ga watan Afrilu, bayan da wani tsohon minista a gwamnatinsa, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo, ya tsere daga gidan yarin na Khartoum .
Ahmed Haroun ya ce shi da wasu tsoffin jami’an gwamnatin Bashir sun tsere daga gidan yarin na Kober a wata sanarwa da aka watsa a tashar talabijin ta Tayba ta Sudan a ranar Talata, 25 ga Afrilu.
Fada ya sake barkewa a Sudan da yammacin jiya Talata duk da sanarwar tsagaita bude wuta da bangarorin da ke gaba da juna suka yi yayin da wasu da dama suka tsere daga Khartoum a cikin rudani.