Tsayin-Dakan ‘Yan Nijar Na Ganin Faransa Ta Janye Dakarunta Daga Kasar


A Jamhuriyar Nijar, Dubban mutane ne ke ci gaba zanga-zanga da zaman dirshen a Yamai babban birnin kasar jiya Asabar, inda suke bukatar Faransa ta gaggauta janye dakarunta daga kasar.
Masu zanga-zangar sun taru a wajen sansanin sojin faransa bisa kiran da kungiyoyi farar hula da dama suka yi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Masu zanga-zangar na dauke da tutoci da kwalaye wadanda aka rubuta “sojojin Faransa ku fita ku bar kasarmu”.
A ranar Juma’a kasar ta Faransa ta yi wasu kalamai inda ta ce a shirye take domin ta mayar da martani idan aka sake kai hari kan dakaru da ma’aikatan diflomasiyyarta da ke aiki a Jamhuriyar Nijar.
Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa ta kara tsami matuka bayan Faransar ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Bazoum, da sojoji suka hambarar a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.
A ranar 3 ga watan Agusta, sojojin na Nijar din sun sanar da warware duk wata yarjejeniya ta soji da Faransa wadda ke da sojoji 1,500 a kasar, matakin da Faransar ta yi watsi da shi, tana mai cewa halastaciyar gwamnatin Bazoum ce kawai ke da ikon yanke wata alaka da su.