September 11, 2021

Tsauraran Matakai Don Dakile Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Canza Salo

Daga Ahmad Muhammad

Matakan da gwamnonin jahohin Arewa ta yamma suka dauka kan yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yan kwanakin baya bayan nan wanda suka hada rufe kasuwanni da hana harkokin yan bumburutu ya shigar da yan bindiga halin tsaka mai wuya musamman a jahar Zamfara.

Amma abin tambaya itace shin hakan zai sanya yan bindigan su mika wuya ga hukuma?
Rahotannin a yan kwanakin nan na nuna yan bindigansun canza salo biyan fansa bayan matsanancin halin da suka tsinci kan su.

A sabili da yunwa da ta addabe su, sun fara neman kayan abinci daga wurin iyalan wanda suka kama a maimakon kudin fansa da suka kasance suna karba a da.

Wani mazaunin garin Sabon Birni ya bada rahoto cewa wasu makobtansa sun fanshi ‘yar su da kayan abinci daga hannun yan bindiga.

Ya bayyana cewa a yayin da iyayen yarinyar ke fafutukar hada kan kudaden fansan yar ta su sai yan bindigan suka nemi su biya wani adadi na shinkafa a matsayin fansan yarinyar.

 

Wani mutum daban daga jahar Sokoto ya sake bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka nemi kayan abinci da lemo don fansar wani direba a jahar.

Ya bayyana cewa sun bukaci a saya musu buhunan shinkafa da lemon karin kuzari fearless da katan katan na taliyar leda (spaghetti) Tabar sigari da kuma aika masu da ragowar canjin. Mutumin ya bayyana cewa har yanzu ana kan hada kudaden ne wanda adadin su yakai kimanin Naira 600,000.

Wani magani a bangaren tsaro mai suna Aminu Bala Sokoto Ya bayyana cewa kokarin da jami’an tsaro suke a Zamfara yana tasiri sannan kuma yana bada sakamakon mai kyau.

Ya nuna cewa luguden wutan da ake bai tsaya akan yan bindigan kadai ba, ya hada har da dakunan ajiyar su, sakamakon haka a halin yanzu suna tsaka mai wuya inda suke gudun neman tsara da rayukan su.

Kana kuma lamarin ya kara tsananta a gare su bayan katse layukan waya da akayi a jahohin Zamfara da Katsina saboda banza su iya riskar yan uwan mutanen da suka yi garkuwa da su ba.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Tsauraran Matakai Don Dakile Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Canza Salo”