July 28, 2021

TOBY YA KAMMALA KOMAWA AL DUHAIL TA QATAR DAGA TOTTENHAM.

TOBY YA KAMMALA KOMAWA AL DUHAIL TA QATAR DAGA TOTTENHAM.

 

Ƙungiyar Ƙwallon ƙafa ta Al Duhail da ke kasar Qatar ta dauki dan wasa Tobi Alderweireld daga Tottenham, Hakan ya kawo karshen kaka shida da dan kwallon tawagar Belgium ya yi a kungiyar da ke buga gasar Premier League.

 

Ba a dai fayyace kudin cinikin ba, amma wasu kafar yada labarai a Burtaniya sun ce Al Duhail ta dauki dan wasan mai shekara 32 kan fam miliyan 13.

 

Alderweireld, wanda ya koma Tottenham daga Atletico Madrid a Yulin 2015, ya yi wa kungiyar Ingila wasa 236. wanda ya tsare baya tare da Jan Vertonghen.

 

Alderweired wanda ya taka leda karkashin koci, Mauricio Pochettino yana daga cikin wadanda suka kai kungiyar ta yi ta biyu a Premier League a 2016-17 da buga wasa biyu a Champions League.

 

Alderweireld, ya buga wa tawagar Belgium karawa 113, ya kuma yi fafatawa hudu a gasar Euro 2020, inda Italiya ta fitar da Belgium a wasan daf da na kusa da na karshe

Daga

Ibrahim Khamis

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “TOBY YA KAMMALA KOMAWA AL DUHAIL TA QATAR DAGA TOTTENHAM.”