Tinubu ya nemi Sojan Nijar su mayar da mulki cikin watanni 9

Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada shawarar mayar da mulki ga gwamnatin rikon kwarya nan da watanni tara kamar yadda ta faru a kasarsa a karshen karni na 20.
Kungiyar hadakar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta kakabawa Nijar takunkumai bayan da dakarun soji suka hambarar da gwamnatin Muhammad Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli. Kana daga baya kungiyar ta yi alwashin kwatar mulkin ta hanyar amfani da karfin Soja sai dai ikirarin bai yi tasiri ba.
A bangare guda rundunar Sojin Nijar ta bayyana cewa zata mayar da gwamnatin ga farar hula cikin shekaru uku.
Tinubu ya bayyana cewa kasar Najeriya ta koma tsarin Dimokradiyya a shekarar 1999 inda Janar Abdulsalami yayi kokarin tabbatar da haka. Ya kuma kara da cewa hakan abu ne wanda zai iya yiwuwa a kasar ta Nijar.