June 2, 2023

Tinubu ya nada Akume da Gbajabiamila  matsayin shugaban  Sakataren gwamnati  da kuma shugaban ma’aikata

 

Shugaban kasan Najeriya Bola Tinubu ya bayyana Sanata George Akuma wanda ya kasance tsohon Ministan ayyuka na musamman a matsayin sabon sakataren gwamnati.

Kana a bangare guda kuma an bayyana tsohon kakakin majalisar dokokin Najeriya Femi Gbajabiamila a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin shugaba Tinubu. A bangare guda kuma Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.

Wannan duk na zuwa ne biyo bayan kokarin sabuwar gwamnatin na raba mukamai a guraben mabambanta a fadin kasar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Tinubu ya nada Akume da Gbajabiamila  matsayin shugaban  Sakataren gwamnati  da kuma shugaban ma’aikata”