August 19, 2023
Tinubu Ya Bai Wa Sabbin Ministoci Ma’aikatun Da Za Su Yi Aiki

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bayyana jerin sunayen ministocin gwamnatinsa, kimanin watanni uku bayan hawansa karagar mulki.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale, bai shaidawa manema labarai ranar da za a rantsar da ministocin ba
Ga jerin kamar haka:
- Babban Ministan Tsaro – Muhammad Badaru
- Karamin Ministan Tsaro – Bello Matawalle
- Karamin Ministan Gidaje da Bunkasar Birane – Abdullahi Gwarzo
- Ministan Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki– Atiku Bagudu
- Ministan Birnin Tarayya – Nyesom Wike
- Karamar Ministar Birnin Tarayya – Mairiga Mahmud
- Ministar Al’adu da Bunkasa Tattalin Arziki – Hannatu Musawa
- Karamin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli – Bello Goronyo
- Ministan Gona da Samar da Abinci – Abubakar Kyari
- Ministan Ilimi – Tahir Mamman
- Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’idu Alkali
- Ministan Harkokin Waje – Yusuf Tuggar
- Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a –Ali Pate
- Ministan Harkokin ‘Yan Sanda – Ibrahim Gaidam
- Karamin Minsitan Tama da Karafa – U Maigari Ahmadu
- Ministan Sadarwa da Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Intanet – Bosun Tijani Ministan Muhalli – Ishak Salako
- Ministan Kudi – Wale Edun
- Ministan Harkokin Teku – Bunmi Tunji
- Ministan Lantarki – Adedayo Adelabu Karamin
- Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a – Tunji Alausa
- Ministan Ma’adanai – Dele Alake
- Ministan Harkokin Yawon Bude Ido – Lola Ade-John
- Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola
- Ministan Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari – Doris Anite
- Ministan Kimiyya da Fasaha – Uche Nnaji
- Karamin Ministan Kwadago da Ayyuka – Nkiruka Onyejeocha
- Ministan Harkokin Mata – Uju Kennedy
- Ministan Ayyuka – David Umahi
- Ministan Matasa – Abubakar Momoh
- Ministan Ayyukan Jin kai da Rage Talauci – Betta Edu
- Karamin Ministan Iskar Gas – Ekperikpe Ekpo
- Ministan Man Fetur – Heineken Lokpobiri
- Ministan Wasanni – John Enoh
- Karamin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sunumu