March 19, 2024

Tinubu ya bada umarnin a farauto masu kashe sojoji a Delta

Tinubu ya bada umarnin a farauto masu kashe sojoji a Delta

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umurci sojojin kasar da su kama wadanda suka kashe sojoji 16 da aka kashe yayin da suke aikin samar da zaman lafiya a kudancin kasar a makon jiya.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce sojojin na mayar da martani ne kan rikicin da ya barke tsakanin al’ummar Okuama da Okoloba a yankin kudancin jihar Delta mai arzikin man fetur, yayin da wasu matasan yankin suka far musu.

Shugaba Tinubu ya ce an kashe farar hula a wani abin da ya kira “harin kai tsaye ga al’ummarmu.”

Shugaban ya ce “Masu aikata wannan danyen aikin  za su fuskanci hukunci ba.”

#Najeriya

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Tinubu ya bada umarnin a farauto masu kashe sojoji a Delta”