September 6, 2023

Tawagar Sudan za ta halarci babban taron MDD karo na 78

Tawagar kasar Sudan karkashin jagorancin shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar kuma babban kwamandan sojojin kasar ta Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, za ta halarci zaman babban taron MDD karo na 78 da zai gudana a birnin New York na kasar Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Talata cewa, ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na kasar, Jibril Ibrahim zai raka Al-Burhan wajen babban taron majalisar.

Tawagar ta kuma hada da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Ali Al-Sadiq, da darektan hukumar leken asirin kasar, Ahmed Ibrahim Mufadel

 

©Cri

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Tawagar Sudan za ta halarci babban taron MDD karo na 78”