April 3, 2024

Tawagar kasar Rasha ta isa birnin Massawa mai tashar jiragen ruwa na kasar Eritiriya

Tawagar kasar Rasha karkashin jagorancin mataimakin kwamandan sojojin ruwa na kasar Vladimir Kasatonov ta isa birnin Massawa mai tashar jiragen ruwa na kasar Eritiriya domin tattaunawa a tsakanin kasashen biyu.

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu manyan jami’an sojin kasar Eritrea karkashin jagorancin babban hafsan sojin kasar Philipos Woldeyohannes da kwamishinan al’adu da wasanni Zemede Tekle suka yi maraba da shi.

Kafafen yada labaran kasar sun bayyana cewa, ziyarar na daga cikin abubuwan da ake bukin cika shekaru 30 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

A yayin ganawar tasu, za a tattauna “batutuwan dake da nasaba da juna,” a cewar gidan talabijin na kasar Eritrea.

Gidan talabijin din ya ce ma’aikatan jirgin ruwan Rasha da ya sauka a tashar ruwa ta Massawa a ranar Alhamis din da ta gabata don ziyarar kwanaki biyar sun zagaya wuraren tarihi a birnin tare da buga wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta sojojin ruwan Eritiriya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Tawagar kasar Rasha ta isa birnin Massawa mai tashar jiragen ruwa na kasar Eritiriya”